Hadisai

Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «مَنْ حَجَّ لِلهِ فَلَمْ يَرْفُثْ وَلَمْ يَفْسُقْ رَجَعَ كَيَوْمِ وَلَدَتْهُ أُمُّهُ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda ya ziyarci Dakin Allah - Madaukakin sarki - da Hajji kuma bai yi kwarkwasaba, kwarkwasa ita ce jima'i da abubuwan dake da alaka da shi na sumbata da runguma, kuma ana ambatansa da mummunanan zance, kuma bai yi fasikanciba, ta hanayar aikata sabo da munanan ayyuka ba, Daga fasikanci akwai aikata abubuwan da ka haramta in an yi harama, zai dawo daga hajjinsa wanda aka gafartawa, kamar yadda ake haifar yaro kubutacce daga zunubai.

Fa'idoji

  • Fasikanci koda ya kasance abin hanawa a kowane lokaci, to hanin yana karfafuwa a aikin hajji dan girmamawa ga ayyukan Hajji.
  • Mutum ana haifarsa ba tare da kurakurai ba kubutacce daga zunubai; to shi ba ya daukar kuskuren waninsa.
Sharhi: العربية

يُبَيِّن النبي صلى الله عليه وسلم أنَّ مَنْ حَجَّ لله تعالى ولم يرفث، والرَّفَث الجماع ومقدماته من التقبيل والمباشرة، ويطلق أيضًا على القول الفاحش، ولم يفسق، بفعل المعاصي والسيئات، ومن الفسوق فعل محظورات الإحرام، رَجع من حَجِّهِ مغفورًا له، كما يولد الصّبِي سالمًا من الذنوب.

  • الفُسُوق وإن كان ممنوعًا في جميع الأحوال، فيتأكد النهيُ عنه في الحج تعظيمًا لمناسك الحج.
  • الإنسان يولد بدون خطايا مُبرَّءًا من الذنوب؛ فهو لا يحمل خطيئة غيره.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari