Hadisai

Cewa an samu wata mace a wasu daga yakokin Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi a kashe, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana kashe mata da yara

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما: أَنَّ امْرَأَةً وُجِدَتْ فِي بَعْضِ مَغَازِي النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَقْتُولَةً، فَأَنْكَرَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَتْلَ النِّسَاءِ وَالصِّبْيَانِ.

Fassara

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Cewa an samu wata mace a wasu daga yakokin Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi a kashe, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana kashe mata da yara.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wata mace an kashe ta a ɗaya daga cikin yake-yake, sai ya yi inkarin kashe mata da kananan yara waɗanda basu isa mafarki ba.

Fa'idoji

  • Wanda bai yi yaki ba cikin mata da yara, da wanda ke cikin hukuncinsu na tsofaffi da masu ibada, domin cewa su ba'a kashe su, muddin dai waɗannan basu kasance daga ma'abota ra'ayi da taimako akan yakar musulmai ba, idan sun kasance hakan to za'a kashe su.
  • Hani akan kashe mata da yara; domin su ba sa yakar musulmai, abin nufi a yaki a tafarkin Allah - Maɗaukakin sarki - (shi ne) karya karfin mayaka kawai; har Da’awar gaskiya ta kai zuwa ga mutane baki ɗaya.
  • Jin kan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - har a fagen yaki.
Sharhi: العربية

رَأى النبيُّ صلى الله عليه وسلم امرأةً مقتولةً في إحدى الغزوات، فأنْكَرَ قَتْلَ النساء والصيبان الصغار الذين لم يبلغوا الحنث.

  • مَن لم يقاتل مِن النساء، والصبيان، ومَن في حُكمهم من الشيوخ الفانِيْن والرهبان، فإنهم لا يُقتَلون، ما لم يكن هؤلاء من أصحاب رأي ومساعدة على قتال المسلمين، فإذا كانوا كذلك فإنهم يُقتلون.
  • النهي عن قتل النساء والصبيان؛ لأن هؤلاء لا يُقاتلون المسلمين، والمقصود من الجهاد في سبيل الله تعالى كَسْر شوكة المقاتلين فقط؛ حتى تصل دعوة الحق إلى الناس أجمعين.
  • رحمة النبي صلى الله عليه وسلم حتى في الغزوات والحروب.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari