Hadisai

ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما: عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ نَهَى عَنِ النَّذْرِ، وَقَالَ: «إِنَّهُ لَا يَأْتِي بِخَيْرٍ، وَإِنَّمَا يُسْتَخْرَجُ بِهِ مِنَ الْبَخِيلِ».

Fassara

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Shi ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci".

Sharhi

Tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga bakance, shi ne mutum ya wajabtawa kansa wani abu wanda shari'a ba ta wajabta masa ba, kuma ya ce: Lallai bakance ba ya gabatar da komai kuma ba ya jinkirtar da shi, kawai ana fitar da shi ne daga marowacin da ba ya aikata komai sai wajibin da ke kansa kawai, kuma bakance ba ya zuwa da abinda ba'a kaddara masa shi ba.

Fa'idoji

  • Ba'a shara'anta bakance ba, sai dai idan ya yi bakance to cika shi ya wajaba idan ba sabo ba ne.
  • Sababi a hanin (cewa shi ba ya zuwa da alheri); domin ba ya juyar da komai daga hukuncin Allah; kuma kada mai bakancen ya yi zatan cewa samun abinda yake nema ya kasance ne da sababin bakancen, Allah - Maɗaukakin sarki - Mawadaci ne daga hakan.
  • Kurɗubi ya ce: Wannan hanin bigiransa misali ya ce: Idan Allah Ya warkar da mara lafiya na to na wajabta wa kaina kaza. Ta yadda karhancin yake shi : yayin da ya tsayar da aikin kusanci akan faruwar abinda yake so, ya bayyana cewa shi niyyar neman kusanci ga Allah - Maɗaukakin sarki - ba ta zama tsantsa ba saboda abinda ya bijiro da shi, kai ya shiga hanyar neman canji, kuma ya bayyanar da shi cewa shi da bai warkar da mara lafiyansa ba, da bai yi sadaka da abinda ya rataya akan warkar da shi ba, wannan shi ne halin marowaci, cewa shi ba ya fitar da wani abu daga dukiyarsa sai da wani canji magaggauci da zai yi kari kan abinda ya fitar a galibi.
Sharhi: العربية

نَهَى صلى الله عليه وسلم عن النذر، وهو أنْ يُوجِبَ الإنسان على نفسه شيئًا لم يُلزِمْه به الشَّارعُ، وقال: بأنّ النذر لا يقدِّم شيئًا ولا يؤخِّره، وإنما يُستخرج به من البخيل الذي لا يفعل إلا الواجب عليه، وأنَّ النذر لا يأتي بشيء لم يكن قد قدِّر له.

  • لا يُشرع النذر، لكن إذا نَذَرَ وَجَب عليه الوفاء به إن لم يكن معصية.
  • العلة في النهي (أنه لا يأتي بخير)؛ لأنه لا يَردُّ من قضاء الله شيئًا؛ ولئلا يَظن الناذِر أن حصول طلبه كان بسبب النذر، والله تعالى غني عن ذلك.
  • قال القرطبي: هذا النهي محلُّه أن يقول مثلًا: إن شفى الله مريضي فعليَّ صدقة كذا، ووجه الكراهة أنه لما وقَف فِعْلَ القُربة المذكور على حصول الغرض المذكور، ظهر أنه لم يَتَمَخَّض له نية التقرُّب إلى الله تعالى لِما صَدَر منه بل سلك فيها مسلك المعاوضة، ويوضِّحه أنه لو لم يشفِ مريضه لم يتصدّق بما علَّقه على شفائه، وهذه حالة البخيل، فإنه لا يُخرج من ماله شيئًا إلا بعوضٍ عاجل يزيد على ما أخرج غالبًا.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari