Hadisai

Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ سَهْلِ بْنِ سَعْدٍ السَّاعِدِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «رِبَاطُ يَوْمٍ فِي سَبِيلِ اللَّهِ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا، وَمَوْضِعُ سَوْطِ أَحَدِكُمْ مِنَ الجَنَّةِ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا، وَالرَّوْحَةُ يَرُوحُهَا العَبْدُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أَوِ الغَدْوَةُ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا».

Fassara

Daga Sahl ɗan Sa'ad al-sa'idi - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, kuma bigiren bulalar ɗayanku a aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, yammacin da bawa zai yi shi saboda Allah ko jijjifi shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa lazimtar gurin da yake tsakanin musulmai da kafirai dan gadin musulmai daga gare su a yini ɗaya yana mai tsarkake niyya saboda Allah, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma bigiren bulalar da zai yi yaƙi da ita saboda Allah a cikin aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma lallai cewa lada da sakamakon tafiya a cikin lokaci daga farkon yini zuwa farkon lokacin azahar, ko yammaci: Daga lokacin azahar zuwa dare saboda Allah sau ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.

Fa'idoji

  • Falalar zaman dako saboda Allah, dan abinda ke cikinsa na sadaukar da rai, dan kuma abinda yake jerantuwa a kansa na ɗaukaka kalmar Allah da taimakon AddininSa; saboda haka lallai sakamakon yini ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
  • Wulaƙantar duniya dangane da lahira; domin cewa gurbin bulala na aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
  • Falalar yaƙi saboda Allah, da girman ladansa; domin ladan yammaci ɗaya ko jijjifi ɗaya shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
  • Faɗinsa; "Saboda Allah" A cikinsa akwai nuni akan muhimmancin tsarkake niyya, kuma cewa lada mai jerantuwa ne a kansa.
Sharhi: العربية

يخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن ملازمة المكان الذي بين المسلمين والكفار لحراسة المسلمين منهم ليوم واحد مُخلصًا لله خير من الدنيا وما فيها، وأن موضع السوط الذي يجاهد به في سبيل الله في الجنة خير من الدنيا وما فيها، وأن أجر وثواب السير في الوقت الذي من أول النهار إلى بداية وقت الظهر، أو الروحة: من وقت الظهر إلى الليل في سبيل الله مرة واحدة، خير من الدنيا وما فيها.

  • فضل الرباط في سبيل الله، لما فيه من المخاطرة بالنفس، ولما يترتب عليه من إعلاء كلمة الله ونصر دينه؛ لذا فإن ثواب يوم واحد، خير من الدنيا وما فيها.
  • حقارة الدنيا بالنسبة للآخرة؛ لأن موضع السوط من الجنة، خير من الدنيا وما فيها.
  • فضل الجهاد في سبيل الله، وعظم ثوابه؛ لأن ثواب الروحة الواحدة أو الغدوة، خير من الدنيا وما فيها.
  • قوله: "في سبيل الله" فيه الدلالة على أهمية الإخلاص، وأن الأجر مترتب عليه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari