Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنين رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا، قَالَتْ: مَا رَأَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مُسْتَجْمِعًا قَطُّ ضَاحِكًا، حَتَّى أَرَى مِنْهُ لَهَوَاتِهِ، إِنَّمَا كَانَ يَتَبَسَّمُ.
Fassara
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Ban taɓa ganin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ƙyaƙyata dariya ba, har inga ƙarshen ganɗarsa ba, kawai ya kasance yana murmushi.
Sharhi
Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai zama mai kai matuƙa a dariya ba har aga ganɗarsa ta sama ba, ita ce naman dake rataye a saman maƙogwaro, kawai ya kasance yana murmushi ne.
Fa'idoji
- Dariyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance murmushi ce idan ya yarda da wani abu ko aka ƙayatar da shi da wani abu.
- Ibnu Hajar ya ce: Ban taɓa ganinsa ba yana ƙyaƙyata dariya ba ta inda zai tayin dariya cikakkiyar dariya mai fuskantowa da gabadayansa akan dariya ba.
- Yawaita dariya da ɗaga murya da ƙyaƙyata dariya bai zama daga siffofin mutanen kirki ba.
- Yawaita dariya yana tafiyar da kwarjinin mutum da kuma nutsuwarsa a tsakanin 'yan uwansa.
Sharhi: العربية
أَخْبَرَتْ عائشةُ رضي الله عنها أنَّ النبيَّ صلى الله عليه وسلم لم يكن مُبالِغًا في الضحك حتى تُرى لَهَاتُهُ، وهي اللَّحْمَة المُتعلِّقة في أعلى الحَلْق، إنما كان يَتَبَسّم.
- كان رسول الله صلى الله عليه وسلم ضَحِكُهُ التبسم إذا رضي أو أُعْجِب بشيء.
- قال ابن حجر: ما رأيته مُستجْمِعًا من جهة الضحك بحيث يضحك ضَحِكًا تامًّا مُقبِلًا بِكُلّيته على الضحك.
- كثرة الضحك وارتفاع الصوت بالقهقهة ليس من صفات الصالحين.
- كثرة الضحك تُذهِب هيبةَ الرجل ووقارَه بين إخوانه.