Hadisai

Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah,

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَن ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَرْفَعُ يَدَيْهِ حَذْوَ مَنْكِبَيْهِ إِذَا افْتَتَحَ الصَّلَاةَ، وَإِذَا كَبَّرَ لِلرُّكُوعِ، وَإِذَا رَفَعَ رَأْسَهُ مِنَ الرُّكُوعِ، رَفَعَهُمَا كَذَلِكَ أَيْضًا، وَقَالَ: «سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، رَبَّنَا وَلَكَ الحَمْدُ»، وَكَانَ لاَ يَفْعَلُ ذَلِكَ فِي السُّجُودِ.

Fassara

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah, haka nan in zai yi kabbara dan ruku'u, haka idan kuma zai ɗago kansa daga ruku'u sai ya ɗagasu, kuma ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gare ka, ya kasance ba ya yin haka a cikin sujjada.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana ɗaga hannayensa agurare uku a sallah, daura da kafaɗa wanda shi ne: Matattarar ƙashin kafaɗa da damtse. Guri na farko: Idan zai buɗe sallah yayin kabbarar harama. Na biyu: Idan Zai yi kabbara dan ruku'u. Na uku: Idan ya ɗago kansa daga ruku'u kuma ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareka. Ya kasance ba ya ɗaga hannayensa a lokacin fara sujjada, ko lokacin ɗagowa daga sujjada.

Fa'idoji

  • Daga hikimomin ɗaga hannaye a cikin sallah cewa hakan ado ne ga sallah da kuma girmama Allah - tsarki ya tabbatar maSa -.
  • Ɗaga hannaye ya tabbata daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - aguri na huɗu a cikin riwayar Abu Humaid al-Sa'idi a wajen Abu Dawud da waninsa, shi ne lokacin tasowa daga tahiyar farko a sallah mai raka'a uku da mai raka'a huɗu.
  • Ya tabbata daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi yana ɗaga hannayensa daura da kunnuwansa ba tare da shafa ba, kamar yadda yake a cikin riwayar Malik ɗan Huwairis a cikin Bukhari da Muslim: "Cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi kabbara yana ɗaga hannayensa har sai ya zo dasu daura da kunnuwansa".
  • Haɗawa tsakanin Tasmi'i da Tahmidi wannan ya keɓanci liman da mai sallah shi kaɗai ne kawai, amma mamu sai ya ce: Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa.
  • Faɗin: "Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa" bayan ruku'u ne kamar yadda ya inganta daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa akwai sigogi huɗu, wannan ɗaya ce daga cikinsu, abin da yafi nutum ya bibiyi wadannan sigogin ya zo da wannan wani lokaci, wani lokacin kuma da wannan.
Sharhi: العربية

كانَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم يرفع يديه في ثلاثةِ مواضع من الصلاة إزاء أو مقابل المنكب الذي هو: مجمع عظم الكتف والعضد. الموضع الأول: إذا افتتح الصلاة عند تكبيرة الإحرام. الثاني: إذا كبّر للركوع. الثالث: إذا رفع رأسه من الركوع وقال: سمع الله لمن حمده ربنا ولك الحمد. وكان لا يرفع يديه عند ابتداء السجود، ولا عند الرفع منه.

  • من حِكَم رفع اليدين في الصلاة أنها زينة للصلاة وتعظيم لله سبحانه.
  • ثبت عنه صلى الله عليه وسلم رفع يديه في موضع رابع كما في رواية أبي حميد الساعدي عند أبي داود وغيره، وهو عند القيام من التشهد الأول في الصلاة الثلاثية والرباعية.
  • ثبت عنه صلى الله عليه وسلم أيضًا أنه يرفع يديه حذو أذنيه دون لمس كما في رواية مالك بن الحويرث في الصحيحين: «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان إذا كبر رفع يديه حتى يحاذي بهما أذنيه».
  • الجمع بين التسميع والتحميد خاص بالإمام والمنفرد، أما المأموم فيقول: ربنا ولك الحمد.
  • قول: "رَبَّنَا وَلَكَ الحَمْدُ" بعد الركوع صح عن النبي صلى الله عليه وسلم فيه أربع صيغ، وهذه واحدة منها، والأفضل أن يتتبع المرء هذه الصيغ ويأتي بهذا مرة، وهذه مرة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari