Hadisai

Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «السَّاعِي عَلَى الأَرْمَلَةِ وَالمِسْكِينِ، كَالْمُجَاهِدِ فِي سَبِيلِ اللَّهِ، أَوِ القَائِمِ اللَّيْلَ الصَّائِمِ النَّهَارَ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake tsayuwa akan al’amuran matar da mijinta ya rasu alhali ba ta da wani wanda zai tsaya akan lamuran ta, da kuma miskini mabukaci, yana ciyar dasu yana mai neman lada a wurin Allah - Madaukakin sarki -, to shi a lada kamar mayakine a tafarkin Allah, ko kamar mai tsayuwa ne a sallar tahajjudin da baya gajiya, mai azimin da ba ya hutawa.

Fa'idoji

  • Kwadaitarwa akan taimamkekeniya da toshe bukatun masu rauni.
  • Ibada ta kunshi kowane aiki na gari, daga ibada akwai kaikawo ga wacce mijinta ya rasu da kuma miskini.
  • Dan Hubaira ya ce: Abin nufi cewa Allah - Madaukakin sarki - Zai tattaro masa ladan mai azimi da mai tsayuwar (dare) alokaci daya; saboda shi ya tsaya ga matar da mijinta ya rasu a matsayin mijinta..., ya kuma tsaya ga miskinin da ya gajiya daga tsayuwa akan kansa, sai ya ciyar da wannan ragowar abincinsa, ya kuma yi sadaka da karfinsa, sai amfaninsa ya zama ya yi daidai da azimi da tsayuwar dare da kuma yaki.
Sharhi: العربية

يُخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ الذي يقوم بمصالِحِ المرأةِ التي مات عنها زوجُها وليس لها أحدٌ يقوم بشؤونِها، والمسكينِ المُحتاج، ويُنفِقُ عليهم محتسبًا الأجرَ عند الله تعالى، فهو في الأجر كالمجاهد في سبيل الله، أو كالقائم في صلاة التهجد الذي لا يَتعب، الصائم الذي لا يفطر.

  • الحثُّ على التعاون والتكافل وسَدّ حاجات الضعفاء.
  • العبادة تشمل كلَّ عمل صالح، ومن العبادة السعي على الأرملة والمسكين.
  • قال ابن هبيرة: والمراد أن الله تعالى يجمع له ثواب الصائم والقائم والمجاهد في دفعة؛ وذلك أنه قام للأرملة مقام زوجها ...، وقام على ذلك المسكين الذي عجز عن قيامه بنفسه، فأنفق هذا فضل قوته، وتصدق بجَلَدِه، فكان نفعه إذًا يكافئ الصوم والقيام والجهاد.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari