Hadisai

‌Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضيَ اللهُ عنهما: أنَّهُ قَالَ لعَطَاءِ بْنِ أَبِي رَبَاحٍ: أَلَا أُرِيكَ امْرَأَةً مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ؟ قُلْتُ: بَلَى، قَالَ: هَذِهِ الْمَرْأَةُ السَّوْدَاءُ، أَتَتِ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَتْ: إِنِّي أُصْرَعُ وَإِنِّي أَتَكَشَّفُ، فَادْعُ اللهَ لِي، قَالَ: «إِنْ شِئْتِ صَبَرْتِ وَلَكِ الْجَنَّةُ، وَإِنْ شِئْتِ دَعَوْتُ اللهَ أَنْ يُعَافِيَكِ» قَالَتْ: أَصْبِرُ، قَالَتْ: فَإِنِّي أَتَكَشَّفُ فَادْعُ اللهَ أَنْ لَا أَتَكَشَّفَ، فَدَعَا لَهَا.

Fassara

Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Cewa shi ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah; Shin bana nuna maka wata mace daga cikin 'yan aljanna ba? na ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar da ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Ni ina farfaɗiya kuma inayin tsirara, to ka roƙamin Allah, ya ce: «‌Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki» ta ce: Zan yi haƙuri, ta ce : To cewa inayin tsirara to ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara, sai ya roƙa mata.

Sharhi

Ibnu Abbas - Allah Ya yarda dasu - ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah: Shin bana nuna maka wata mata daga cikin 'yan aljanna ba? Aɗa'u ya ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar mutuniyar Habasha, ta zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Lallai cewa ni ina da cutar farfaɗiya kuma cewa ni ina yin tsirara wani abu yana yayewa daga jikina alhali ni ban sani ba, to ka roƙamin Allah Ya yaye mini, ya ce: Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki, ta ce: To zan yi haƙurin, sannan ta ce: To ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara idan na yi farfaɗiya, sai ya roƙa mata Allah.

Fa'idoji

  • Haƙuri akan bala'i a duniya yana gadar da aljanna.
  • Nawawi ya ce: A cikin sa akwai dalili akan cewa farfaɗiya ana bada lada a kanta mafi cikar lada.
  • Kamewa da kunyar matan sahabbai, da kuma kwaɗayinsu akan suturta - Allah Ya yarda da su -, wannan matar ta kasance mafi yawan abinda take jin tsoro shi ne wani abu ya yaye daga jikinta.
  • Ibnu Hajar ya ce: Lallai yin riƙo da tsanani shi yafi daga yin riƙo da rangwami ga wanda ya san cewa akan kansa zai iya, kuma ba zai yi rauni ba saboda lazimtar tsanani.
  • Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa cewa maganin cututtuka gaba ɗayansu shi ne addu'a da kuma komawa zuwa ga Allah ya fi tasiri kuma ya fi amfani daga magani da ƙwayoyi, kuma cewa tasirin hakan da kuma tasirin jiki daga gare shi ya fi girma daga tasirin magungunan jiki, sai dai kaɗai yana tasiri ne da al'amura biyu: Na farkonsu ta ɓangaren wanda illar ta sama shi ne gaskiyar nufi, ɗayan kuma ta ɓangaren mai yin maganin, shi ne ƙarfin niyya da kuma ƙarfin zuciyarsa da tsoron Allah da kuma dogara, Allah ne Mafi sani.
  • Ibnu Hajar ya ce; A cikinsa akwai dalili akan halaccin barin yin magani.
Sharhi: العربية

قال ابن عباس رضي الله عنهما لعطاء بن أبي رباح: ألا أريك امرأة من أهل الجنة؟ قال عطاء: بلى، قال: هذه المرأة الحبشية السوداء، أتت النبي صلى الله عليه وسلم، قالت: إن بي مرض فأصرع وإني أتكشف ويظهر شيء من جسدي وأنا لا أشعر، فادع الله أن يعافيني، قال: إن شئت صبرت ولك الجنة، وإن شئت دعوت الله أن يعافيك، قالت: أصبر إذن، ثم قالت: فادع الله أن لا أتكشف إن صرعت، فدعا الله لها.

  • الصبر على البلاء في الدنيا يورث الجنة.
  • قال النووي: وفيه دليل على أن الصرع يثاب عليه أكمل ثواب.
  • عفة وحياء نساء الصحابة، وحرصهن على الستر، رضي الله عنهن، فهذه المرأة كانت أكثر ما تخشاه أن ينكشف شيءٌ من جسمها.
  • قال ابن حجر: أن الأخذ بالشدة أفضل من الأخذ بالرخصة لمن علم من نفسه الطاقة ولم يضعف عن التزام الشدة.
  • قال ابن حجر: وفيه أن علاج الأمراض كلها بالدعاء والالتجاء إلى الله أنجع وأنفع من العلاج بالعقاقير، وأن تأثير ذلك وانفعال البدن عنه أعظم من تأثير الأدوية البدنية، ولكن إنما ينجع بأمرين: أحدهما من جهة العليل وهو صدق القصد، والآخر من جهة المداوي، وهو قوة توجهه وقوة قلبه بالتقوى والتوكل، والله أعلم.
  • قال ابن حجر: فيه دليل على جواز ترك التداوي.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari