Hadisai

Idan ɗayanku ya isa zuwa ga majalisa to ya yi sallama, idan kuma yana so ya tashi to ya yi sallama, domin (sallama) ta farkon bata fi mafi cancanta daga ta ƙarshe ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Hasan neAbu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا انْتَهَى أَحَدُكُمْ إِلَى الْمَجْلِسِ فَلْيُسَلِّمْ، فَإِذَا أَرَادَ أَنْ يَقُومَ فَلْيُسَلِّمْ، فَلَيْسَتِ الْأُولَى بِأَحَقَّ مِنَ الْآخِرَةِ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya isa zuwa ga majalisa to ya yi sallama, idan kuma yana so ya tashi to ya yi sallama, domin (sallama) ta farkon bata fi mafi cancanta daga ta ƙarshe ba".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da wanda ya zo wurin zaman mutane da ya yi musu sallama, idan kuma ya yi nufin ya tashi daga wurin to ya yi wa mutanen wurin bankwana da yin sallama; dan sallamar farkon lokacin zuwa ba ta fi mafi cancanta daga ɗayar sallamar a lokacin da zai bar wurinba.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa akan yaɗa sallama.
  • Kwaɗaitarwa akan yin sallama ga mutanen dake zaune a lokacin haɗuwa da kuma lokacin juyawa.
  • Sindi ya ce: Faɗinsa: (Idan ya yi nufin tashi) wato: Daga majalisar. (To ta farkon bata kasance mafi cancanta ba) wato: Su biyun gaba ɗayansu sunnah ne da yin aiki da su, dan haka babu wata fuska ga barin ta biyu tare da tabbatar data farkon.
Sharhi: العربية

أَرشدَ النبي صلى الله عليه وسلم من جاء لمكان جلوس الناس أن يُسلّم عليهم، فإذا أراد أن يقوم منه فليودع أهله أيضًا بالسلام؛ فليس السلام الأول عند المجيئ بأحق من السلام الآخر عند المغادرة.

  • الحث على إفشاء السلام.
  • الحث على التسليم على أهل المجلس عند اللقاء وعند الانصراف.
  • قال السندي: قوله (وإذا أراد أن يقوم) أي: من المجلس، (فليس الأول بأحق) أي: هما جميعًا سنةٌ حقيقةٌ بالعمل بها، فلا وجه لترك الثاني مع إثبات الأول.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari