Hadisai

SIFFAR WANKAN JANABA

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ مَيْمُونَةُ أُمِّ المؤمِنينَ رضي الله عنها قَالتْ: وَضَعْتُ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ غُسْلًا، فَسَتَرْتُهُ بِثَوْبٍ، وَصَبَّ عَلَى يَدَيْهِ، فَغَسَلَهُمَا، ثُمَّ صَبَّ بِيَمِينِهِ عَلَى شِمَالِهِ، فَغَسَلَ فَرْجَهُ، فَضَرَبَ بِيَدِهِ الأَرْضَ، فَمَسَحَهَا، ثُمَّ غَسَلَهَا، فَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ، وَغَسَلَ وَجْهَهُ وَذِرَاعَيْهِ، ثُمَّ صَبَّ عَلَى رَأْسِهِ وَأَفَاضَ عَلَى جَسَدِهِ، ثُمَّ تَنَحَّى، فَغَسَلَ قَدَمَيْهِ، فَنَاوَلْتُهُ ثَوْبًا فَلَمْ يَأْخُذْهُ، فَانْطَلَقَ وَهُوَ يَنْفُضُ يَدَيْهِ.

Fassara

Daga Maimuna Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Na ajiye wa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ruwan wanka, sai na kare shi da tufafi, sai ya saka a hannayensa, sai ya wankesu, sannan ya zuba da damansa akan hagunsa, sai ya wanke gabansa, sai ya goga hannunsa a kasa, sai ya shafe shi, sannan ya wanke shi, sai ya kuskure baki ya shaƙi ruwa, ya wanke fuskarsa da zira'in hannunsa biyu, sannan ya zuba a kansa sai ya kwaranyo ruwan akan jikinsa, sannan sai ya gusa kadan, sai ya wanke diga-digansa, sai na ba shi tufafi bai karɓa ba, sai ya tafi alhali yana kakkaɓe hannayensa.

Sharhi

Uwar muminai Nana Maimuna - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari game da siffar wankan annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - na tsarki, lokacin da ta ajiye masa ruwa dan ya yi wanka da shi, kuma ta kare shi da labule, sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikata abinda ke tafe: N farko: Ya zuba ruwa a hannayensa sai ya wanke su kafin ya shigar da su cikin abin wanka. Na biyu: Ya zuba ruwa da hannunsa na dama akan hannunsa na hagu sai ya wanke gabansa; dan tsarkake shi daga abinda ya maƙale na alamar janaba. Na uku: Ya bugi ƙasa da hannunsa sai ya shafe shi sannan ya wanke shi dan ya gusar da ƙazanta daga gare shi. Na huɗu: Ya kurkure baki; ta hanyar shigar da ruwa a cikin bakinsa ya motsa shi ya kuma kurkure shi sannan ya zubar da shi, sai ya shaƙi ruwa; ta hanyar da ya shigar da ruwa a cikin hancinsa da nunfashinsa, sannan ya fitar da shi dan ya tsarkake shi. Na biyar: Ya wanke fuskarsa da zira'insa biyu. Na shida: Ya zuba ruwa a kansa. Na bakwai: Ya zuba ruwa a sauran jikinsa. Na takwas: Ya juya daga gurinsa sai ya wanke diga-digansa a wani wurin daban ta inda bai wankesu ba kafin nan. Sannan ta kawo masa wani mayafi dan ya tsane da shi, bai karɓa ba, sai ya fara shafe ruwan jikinsa da hannunsa yana karkaɗe shi.

Fa'idoji

  • Himmatuwar matan annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - da siffanta mafi tsirfafan bayanan rayuwarsa; dan sanar da al'ummarsa.
  • Wannan siffar wankan ɗaya ce daga cikin siffofin da suka tabbata daga annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - a cikin siffar cikakken wanka na janaba, amma siffa mai isarwa to ita ce ya game jikinsa da ruwa tare da kurkure baki da shaƙa ruwa.
  • An halatta tsane jiki da mayani ko a bar shi bayan wanka ko alwala.
Sharhi: العربية

أَخْبرتْ أم المؤمنين ميمونة رضي الله عنها عن صفة اغتسال النبي صلى الله عليه وسلم من الجنابة، حيث وضعت له ماءً ليغتسل به، وسترتْه بساتر، ففعل النبي صلى الله عليه وسلم ما يلي: أولًا: صب الماء على يديه فغسلهما قبل أن يدخلهما الإناء. ثانيًا: صب الماء بيده اليمنى على اليسرى فغسل فرجه؛ لتنظيفه مما علق به من أثر الجنابة. ثالثًا: ضرب بيده الأرض فمسحها ثم غسلها ليزيل الأذى عنها. رابعًا: تمضمض؛ بأن أدخل الماء في فمه وحركه وأداره ثم ألقاه، واستنشق؛ بأن أدخل الماء في أنفه بِنَفَسِهِ، ثم أخرجه لينظفه. خامسًا: غسل وجهه وذراعيه. سادسًا: صب الماء على رأسه. سابعًا: صب الماء على بقية جسده. ثامنًا: تحوّل من مكانه فغسل قدميه في مكان آخر حيث لم يغسلهما من قبل. ثم أتته بخرقة ليتنشف بها، فلم يأخذها، وجعل يمسح الماء عن جسده بيده وينفضه.

  • اهتمام أزواج النبي صلى الله وعليه وسلم بوصف أدقّ تفاصيل حياته؛ تعليمًا للأمة.
  • صفة الغسل هذه هي إحدى الكيفيات التي ثبتت عن النبي صلى الله عليه وسلم في صفة الاغتسال الكامل من الجنابة، وأما الصفة المجزئة فهي أن يعم بدنه بالماء مع المضمضة والاستنشاق.
  • تنشيف الجسد بخرقة أو تركه بعد الغسل أو الوضوء مباح.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari