Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤمنين رضي الله عنها قَالَتْ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا اغْتَسَلَ مِنَ الجَنَابَةِ، غَسَلَ يَدَيْهِ، وَتَوَضَّأَ وُضُوءَهُ لِلصَّلاَةِ، ثُمَّ اغْتَسَلَ، ثُمَّ يُخَلِّلُ بِيَدِهِ شَعَرَهُ، حَتَّى إِذَا ظَنَّ أَنَّهُ قَدْ أَرْوَى بَشَرَتَهُ، أَفَاضَ عَلَيْهِ المَاءَ ثَلاَثَ مَرَّاتٍ، ثُمَّ غَسَلَ سَائِرَ جَسَدِهِ، وَقَالَتْ: كُنْتُ أَغْتَسِلُ أَنَا وَرَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ إِنَاءٍ وَاحِدٍ، نَغْرِفُ مِنْهُ جَمِيعًا.
Fassara
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi wankan janaba, sai ya wanke hannayensa, ya yi alwala alwalarsa domin sallah, sannan ya yi wanka, sannan ya tsettsefe gashinsa da hannunsa har sai ya tabbar cewa ya jika fatarsa, sai ya zuba ruwa akansa sau uku, sannan ya wanke ragowar jijkinsa. Ta ce: Na kasance ina wanka ni da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga kwarya daya muna kanfatowa daga gareta gaba daya.
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin wankan janaba sai ya fara wanke hannayensa, sannna ya yi alwala kamar yadda yake alwalar sallah, sannan ya zuba ruwa a jikinsa, sannan ya tsattsefe gashin kansa da hannayensa, har sai ya tabbar cewa ruwa yakai tushen gashin, ya jika fatar, sai ya zuba ruwa akansa sau uku sannan ya wanke ragowar jijkinsa. Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Na kasance ina wanka ni da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kwarya daya, muna kanfatowa daga gareta gaba daya.
Fa'idoji
- Wanka (Wankan tsarki) nau'i biyu ne: Mai isarwa da kuma cikakke, amma mai isarwa sai mutum ya yi niyyar tsarki, sannan ya game jikinsa da ruwa tare da kuskurar baki da shaka ruwa. Amma cikakken wanka sai ya yi wanka kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wanka a wannan hadisin.
- Ana anfani da lafazin janaba ga dukkanin wanda ya fitar da maniyyi, ko ya tara da matarsa koda bai yi maniyyi ba.
- Halaccin kallon daya daga ma'aurata al'aurar dayan, da kuma wankansu daga kwarya daya.
Sharhi: العربية
كانَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم إذا أراد الغسل من الجنابة بَدأ بغسل يديه، ثم يتوضأ كما يتوضأ للصلاة، ثم يُفيضُ الماءَ على جسدِه، ثم يُخَلِّلُ شَعَرَ رأسِه بيديه، حتى إذا ظَنَّ أنه وَصَلَ الماءُ إلى أُصُولِ الشعر، وأروى البَشَرةَ، صَبَّ الماءَ على رأسِهِ ثلاثَ مَرَّات ثم غَسَلَ باقي جسدِه. وقالتْ عائشةُ رضي الله عنها: كنتُ أَغْتَسِلُ أنا ورسولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم مِنْ إِنَاءٍ واحدٍ، نَغْرِفُ منه جميعًا.
- الغسل نوعان: مُجْزِئٌ وكامِلٌ، أمَّا الغسلُ المُجزئ فيَنْوي الإنسانُ الطهارةَ، ثم يُعَمِّمُ جسدَه بالماءِ مع المضمضةِ والاستنشاق، وأمَّا الغسل الكامل فيَغتَسل كما اغتسل النبي صلى الله عليه وسلم في هذا الحديث.
- تطلق الجنابة على كل مَن أَنْزَل المَنِيَّ، أو جامَعَ ولو لم ينزل.
- جواز نظر أحد الزوجين لعورة الآخر، وغسلهما من إناء واحد.