Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَتَتَّبِعُنَّ سَنَنَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ، شِبْرًا بِشِبْرٍ، وَذِرَاعًا بِذِرَاعٍ، حَتَّى لَوْ دَخَلُوا فِي جُحْرِ ضَبٍّ لَاتَّبَعْتُمُوهُمْ» قُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ آلْيَهُودَ وَالنَّصَارَى؟ قَالَ: «فَمَنْ؟».
Fassara
Daga Abu Sa'id al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai za ku bi hanyoyin waɗanda zo kafinku, taki da taki, zira'i da zira'i, har da ko sun shiga ramin damo ne sai kun bi su" Muka ce: Ya manzon Allah ! Yahudawa da Nasara? ya ce: "To su wa?".
Sharhi
(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana bada labarin abinda halin da sashin al'ummarsa zasu kasance akansa bayan zamaninsa, shi ne bin hanyar Yahudawa da Nasara a aƙidunsu da ayyukansu da al'adunsu bi na zirfafawa mai tsanani taki da taki, zira'i da zira'i, har da a ce su shiga ramin damo to da waɗannan zasu shige shi suna bayansu.
Fa'idoji
- Alama daga alamomin annabtarsa inda ya bada labari da hakan kafin afkuwarsa sai ya afku kamar yadda ya bada labari.
- Hani daga kamanceceniyar musulmai da kafirai, daidai ne a cikin aƙidunsu ne ko ibadunsu ko bukukuwansu ko adonsu wanda ya keɓanta da su.
- Bayyana abubuwa na ma'ana da misalai da ake gani yana daga hanyoyin koyarwa a cikin muslunci.
- Damo; Wata dabba ce raminsa mai tsananin duhu ne mai wari, yana daga dabbobi masu jan ciki yana da yawa a sahara, kuma ta yadda aka keɓance ramin damo: Tsananin ƙuncinsa da muninsa, tare da hakan cewa su - saboda bin su ga sawunsu da bin hanyoyinsu - da ace (Yahudu da Nasara) zasu shiga misalin wannan ƙuncin mai muni da su ma sun bi su! Allah ne abin neman taimako.
Sharhi: العربية
يُخبِرُ صلى الله عليه وسلم بما يكون عليه حال بعض أمته بعد زمانه، وهي متابعة طريقة اليهود والنصارى في عقائدهم وأفعالهم وعاداتهم وتقاليدهم متابعة دقيقة شديدة شبرًا بشبرٍ، وذراعًا بذراعٍ، حتى لو دخلوا جحر ضب لدخله هؤلاء وراءهم.
- علمٌ من أعلام نبوَّته حيث أخبر بذلك قبل وقوعه فوقع كما أخبر.
- النهي عن تشبُّه المسلمين بالكفار، سواء في عقائدهم أو عباداتهم أو أعيادهم أو أزيائهم الخاصة بهم.
- توضيح الأشياء المعنوية بالأمثلة الحسية من أساليب التعليم في الإسلام.
- الضب: حيوان جحره شديد الظلمة نَتِنُ الريح، وهو من الزواحف يكثر في الصحاري، ووجه التخصيص بجحر الضب: شدة ضيقه ورداءته، ومع ذلك فإنهم -لاقتفائهم آثارهم واتباعهم طرائقهم- لو دخلوا في مثل هذا الضيق الرديء لوافقوهم! والله المستعان.