Hadisai

‌Wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗannan 'ya'ya matan, sai ya kyautata musu, zasu zama kariya gare shi daga wuta

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَن عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمِنين رضي الله عنها زَوْجَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حَدَّثَتْهُ قَالَتْ: جَاءَتْنِي امْرَأَةٌ مَعَهَا ابْنَتَانِ تَسْأَلُنِي، فَلَمْ تَجِدْ عِنْدِي غَيْرَ تَمْرَةٍ وَاحِدَةٍ، فَأَعْطَيْتُهَا فَقَسَمَتْهَا بَيْنَ ابْنَتَيْهَا، ثُمَّ قَامَتْ فَخَرَجَتْ، فَدَخَلَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَحَدَّثْتُهُ، فَقَالَ: «مَنْ يَلِي مِنْ هَذِهِ البَنَاتِ شَيْئًا، فَأَحْسَنَ إِلَيْهِنَّ، كُنَّ لَهُ سِتْرًا مِنَ النَّارِ».

Fassara

Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta ce: Wata mata ta zo a tare da ita akwai 'ya'yanta biyu mata, bata samu komai awurina ba banda wani dabino ɗaya, sai na bata shi sai ta raba shi tsakanin 'ya'yan nata mata biyu, sannan ta tashi sai ta fita, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo sai ta zantar da shi, sai ya ce: «‌Wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗannan 'ya'ya matan, sai ya kyautata musu, zasu zama kariya gare shi daga wuta».

Sharhi

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa wata mata ta zo mata a tare da ita akwai 'ya'yanta biyu mata tana tambayarta ta bata abinda zata ci, Nana A'isha bata samu komai a wurinta ba banda dabino ɗaya, sai ta bata shi sai matar ta raba dabinon tsakanin 'ya'yan nata mata biyu ba ta ci komai daga gare shi ba, sannan ta tashi sai ta fita, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga (gida) sai Nana A'isha ta zantar da shi, sai ya ce: Duk wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗanan 'ya'ya matan, sai ya kyauata musu ya tarbiyantar da su ya ciyar da su ya shayar da su ya tufatar da su kuma ya yi haƙuri akan haka, zasu zama sutura da kariya gare shi daga wuta.

Fa'idoji

  • Kula da 'ya'ya mata da kuma ƙoƙari garesu yana daga cikin mafificin ayyukan alheri masu nisantarwa daga wuta.
  • An so yin sadaka da abinda mutum yake da iko a kansa koda ya zama kaɗan ne.
  • Tsananin tausayin iyaye ga 'ya'yayensu.
  • Bayanin halin ɗakunan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa arziƙinsa ya zama tsakatsakiya ne (ya ishe shi).
  • Bayanin falalar fifita wani akan kai kuma cewa hakan yana daga cikin alamomin muminani; haƙiƙa Nana A'isha - Allah Yarda da ita - ta fifita waccan matar da 'ya'yanta biyu akan kanta, wannan yana nuni akan kyautarta da kuma karamcinta tare da tsananin buƙatuwarta.
  • An ambaci kyautar 'ya'ya mata da jarraba; saboda abinda ke cikin renonsu na wahala da gajiya, ko saboda wasu mutane suna ƙin su, ko domin cewa yana rinjaya cewa basu da wata hanya ta samun kuɗi da kuma rayuwa.
  • Musulunci ya zo yana mai tunɓuke al'adun Jahiliyya munana, daga cikin hakan shi ya yi wasicci da 'ya'ya mata.
  • (Mutum) zai iya samun wannan ladan ko da ta kasance 'ya ɗaya ce kamar yadda ya zo a cikin wasu daga cikin ruwayoyi.
Sharhi: العربية

أخبرت أم المؤمنين عائشة رضي الله عنها أن امرأة جاءتها ومعها ابنتان لها تسألها أن تعطيها ما يؤكل، فلم تجد عائشة عندها غير تمرة واحدة، فأعطتها إياها فقسمت المرأة التمرة بين ابنتيها ولم تأكل منها شيئاً، ثم قامت فخرجت، فدخل النبي صلى الله عليه وسلم فحدثته عائشة، فقال: من ولي من هذه البنات شيئًا، فأحسن إليهن وأدبهن وأطعمهن وسقاهن وكساهن وصبر على ذلك، كن له سترًا وحجابًا من النار.

  • رعاية البنات والسعي عليهن من أفضل أعمال البر المجنبة من النار.
  • استحباب التَّصدق بِمَا يقدِر عليه الإنسان ولو كان يسيرًا.
  • شِدَّة عَطْف الأبوين على أبنَائِهِما.
  • بيان حال بيوتات رسول الله صلى الله عليه وسلم وأن رزقه كان كفافًا.
  • بيان فضل الإيثار وأنه من سمات المؤمنين؛ فقد آثرت عائشة رضي الله عنها تلك المرأة وابنتيها على نفسها، وهذا يدل على سخائها وكرمها مع شدة حاجتها.
  • سميت هبة الإناث ابتلاء؛ لما في كفالتهن من المشقة والتعب، أو لكره بعض الناس لهن، أو لأنه يغلب ألّا يكن لهن مورد كسب وعيش.
  • جاء الإسلام باجتثاث عادات الجاهلية المنكرة، ومن ذلك أنه أوصى بالبنات.
  • يحصل على هذا الأجر ولو كانت بنتًا واحدة كما جاء في بعض الروايات.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari