Hadisai

Shin ana taimakonku ne ko ana azurtaku sai saboda raunananku

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ مُصْعَبِ بْنِ سَعْدٍ قَالَ: رَأَى سَعْدٌ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ لَهُ فَضْلًا عَلَى مَنْ دُونَهُ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «هَلْ تُنْصَرُونَ وَتُرْزَقُونَ إِلَّا بِضُعَفَائِكُمْ».

Fassara

Daga Mus'ab ɗan Sa'ad ya ce: Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ga cewa shi yana da wata falala akan wanda ke ƙasa da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin ana taimakonku ne ko ana azurtaku sai saboda raunananku".

Sharhi

Sa'ad ɗan Abu Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya yi zatan cewa shi yana da wata falala akan wanda ke ƙasa da shi daga raunana saboda gwarzantakarsa da makamancin haka! Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Shin ana taimakonku ne kuma ana azirtaku ai sai saboda raunananku ta hanyar addu'o'insu da sallalolinsu da ikhlasinsu; domin su a galibi su ne mafi tsananin ikhlasi a cikin addu'a, kuma mafi yawan khushu'i a cikin ibada dan wofintar zuciyarsu daga rataya da ƙawace-ƙawacen duniya.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa akan tawali'u da hana rena wasu daban.
  • Ibnu Hajar ya ce: Idan mai ƙArgo yana rinjaya saboda gwarzantakara, to shi mai rauni yana rinjaya saboda falalar addu'arsa da kuma ikhlasinsa.
  • Kwaɗaitarwa akan kyautatawa talakawa da basu haƙƙoƙinsu, domin hakan yana daga sabubban rahamar Allah gareka da kuma taimakonSa.
Sharhi: العربية

ظن سعد بن أبي وقاص رضي الله عنه أن له فضلًا على من دونه من الضعفاء بسبب شجاعته ونحو ذلك! فقال صلى الله عليه وسلم: هل تنصرون وترزقون إلا بضعفائكم بدعواتهم وصلاتهم وإخلاصهم؛ فهم غالبًا أشد إخلاصًا في الدعاء، وأكثر خشوعًا في العبادة لخلاء قلوبهم عن التعلق بزخرف الدنيا.

  • الحض على التواضع ومنع الترفُّع على الآخرين.
  • قال ابن حجر: إن كان القوي يترجح بفضل شجاعته، فإن الضعيف يترجح بفضل دعائه وإخلاصه.
  • الحث على الإحسان إلى الفقراء وإعطائهم حقوقهم، فإن ذلك من أسباب رحمة الله لك ونصره.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari