Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: كُنَّا مَعَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، إِذْ سَمِعَ وَجْبَةً، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تَدْرُونَ مَا هَذَا؟» قَالَ: قُلْنَا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «هَذَا حَجَرٌ رُمِيَ بِهِ فِي النَّارِ مُنْذُ سَبْعِينَ خَرِيفًا، فَهُوَ يَهْوِي فِي النَّارِ الْآنَ حَتَّى انْتَهَى إِلَى قَعْرِهَا».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yayin da ya ji wata kara, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin kun san mene ne wannan?" ya ce: Muka ce: Allah da ManzonSa ne mafi sani, ya ce: "Wannan wani dutsene da aka jefa shi cikin wuta tun shekara saba'in, shi (dutsan) yana faɗawa cikin wuta a yanzu, har sai da ya kai karshanta".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji wani sauti (kara) mai tsoratarwa kamar faɗuwar wani jiki daga jikkuna, sai ya tambayi waɗanda ke tare da shi cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - game da wannan karar, sai suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai wanann karar da kuka ji ta ta wani dutse ce da aka yi jifa da shi daga gefen Jahannama tun shekara saba'in, shi yana sauka yana faɗawa a cikinta, har sai ya kai karshenta a yanzu lokacin da kuka ji sautin.
Fa'idoji
- Kwaɗaitarwa akan tanadi ga ranar lahira da aiki na gari, da gargaɗarwa daga Jahannama.
- An so danganta ilimi zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - cikin abinda babu wani sani ga mutum akan shi.
- Zaburar da malami himmatuwa da faɗaka kafin yin bayani; dan ya zama mafi jawo hankali wurin fahimtarwa.
Sharhi: العربية
سَمِعَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم صوتًا مُزْعِجًا كسقوطِ جسمٍ من الأجسام، فسأل مَن عنده من الصحابة رضي الله عنهم عن ذلك الصوت، فقالوا: الله ورسوله أعلم. فقال لهم صلى الله عليه وسلم: إنَّ هذا الصوت الذي سمعتموه هو لحَجَرٍ رُمي به من شَفِيْر جهنم منذ سبعين عامًا، فهو يهوي ويسقط فيها، حتى انتهى إلى قَعرِها الآن حين سمعتم الصوت.
- الحث على الاستعداد لليوم الآخر بالعمل الصالح، والتحذير من جهنم.
- استحباب إسناد العلم إلى الله تعالى فيما لا علم للإنسان به.
- إثارة المعلّم الاهتمام والانتباه قبل البيان؛ ليكون أدعى إلى الإفهام.