Hadisai

Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin ladaddakin wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga ladansu ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ دَعَا إِلَى هُدًى كَانَ لَهُ مِنَ الْأَجْرِ مِثْلُ أُجُورِ مَنْ تَبِعَهُ، لَا يَنْقُصُ ذَلِكَ مِنْ أُجُورِهِمْ شَيْئًا، وَمَنْ دَعَا إِلَى ضَلَالَةٍ كَانَ عَلَيْهِ مِنَ الْإِثْمِ مِثْلُ آثَامِ مَنْ تَبِعَهُ، لَا يَنْقُصُ ذَلِكَ مِنْ آثَامِهِمْ شَيْئًا».

Fassara

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin ladaddakin wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga ladansu ba, wanda ya yi kira zuwa ga bata yana da zunubi kwatankwacin zunuban wadanda suka bi shi, ba za’a tauye komai daga zunubansu ba".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya shiryar ya kwadaitar da mutane kan hanyar da aciknta akwai gaskiya da alheri da fada ne ko aikatawa yana da ladan wanda ya bi shi ba tare da antauye komai daga ladan mai bin ba. Wanda ya kira mutane zuwa hanyar karya da sharri a cikinta akwai zunubi da kuskure ko wani al'amarin da ba ya halatta, na fadane ko aikatawa, ya kasance akwai zunubi akansa kwatankwacin zunubin wanda ya bi shi ba tare da an tauye komai daga zunubansu ba.

Fa'idoji

  • Falalar kira zuwa shiriya, kadan ce ko da yawa, kuma cewa mai kira yana da ladan mai aikin, hakan yana daga girman falalar Allah da cikar karamcinSa.
  • Hadarin kira zuwa ga bata kadan ce ko da yawa, kuma mai kiran yana da zununubi kwatankwacin zunubin wanda ya aikata.
  • Sakamako yana daga jinsin aiki, wanda ya yi kira zuwa alheri yana da ladan wanda ya aikata shi, wanda ya yi kira zuwa ga sharri yana da zunubi kwatankwacin zunubin wanda ya aikata shi.
  • Ya wajaba akan musulmi ya kiyayi a yi koyi da shi dan bayyanar da sabonsa ga mutane suna kallonsa, cewa shi zai yi laifi da wanda ya kwaikwayeshi koda bai zaburar da shi akan hakan ba.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن أَرشَدَ وَدَلَّ وحَضَّ الناسَ على طريقٍ فيه حقٌّ وخيرٌ بقولٍ أو فعلٍ كان له مِثْلُ أجرِ مَن تَبِعَه دون أنْ ينقص ذلك من أجر التابع شيئًا. ومَن أَرشَدَ ودَلَّ الناسَ إلى طريقِ باطلٍ وشرٍّ فيه ذنب وخطيئة أو أمر لا يَحِلّ، بقول أو فعل، كان عليه مِثْلُ وِزْرِ وإِثمِ مَن تَبِعَه مِن غير أن ينقص ذلك من آثامِهِم شيئًا.

  • فضل الدعوة إلى الهدى، قليلًا كان أو كثيرًا، وأنَّ الدّاعي له مِثلُ أجر العامل، وذلك من عظيم فضل الله وكمال كرمه.
  • خطورة الدعوة إلى الضلال، قليلًا كان أو كثيرًا، وأنّ الداعي عليه مِثل وِزْر العامل.
  • الجزاء من جنس العمل، فمن دعا إلى الخير كان له مثل أجر فاعله، ومن دعا إلى الشر كان عليه مثل وزر فاعله.
  • على المسلم أن يَحذَرَ مَن أن يُقتَدَى به بمجاهرته بالمعصية والناس يَرونه، فإنه يأثم بِمَن قَلَّدَه ولو لم يَحُثَّه على ذلك.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari