Hadisai

Wanda ya mutu alhali shi yana kiran kishiya wanin Allah zai shiga wuta

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قال: قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم كَلِمَةً وَقُلْتُ أُخْرَى، قَالَ النَّبِيُّ صلى الله عليه وسلم: «مَنْ مَاتَ وَهُوَ يَدْعُو مِنْ دُونِ اللهِ نِدًّا دَخَلَ النَّارَ» وَقُلْتُ أَنَا: مَنْ مَاتَ وَهُوَ لَا يَدْعُو لِلهِ نِدًّا دَخَلَ الْجَنَّةَ.

Fassara

Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadi wata kalma ni kuma na fadi wata daban, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mutu alhali shi yana kiran kishiya wanin Allah zai shiga wuta" Ni kuma na ce: Wanda ya mutu alhali shi ba ya kiran kishiya ga Allah zai shiga aljanna.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bamu labarin cewa wanda ya karkatar da wani abu daga abinda yake wajaba ya zama na Allah ne zuwa waninSa, kamar rokon wanin Allah - Madaukakin sarki - ko neman agaji ga waninSa, ya kuma mutu akan hakan to cewa shi yana daga 'yan wuta. Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya kara cewa wanda ya mutu alhali ba ya hada wani abu da Allah to makomarsa tana aljanna.

Fa'idoji

  • Addu'a ibada ce ba'a yinta sai ga Allah - Madaukakin sarki -.
  • Falalar tauhidi, kuma cewa wanda ya mutu akansa zai shiga aljanna, koda an yi masa azaba akan sashin zunubai.
  • Hadarin shirka, kuma cewa wanda ya mutu akanta zai shiga wuta.
Sharhi: العربية

يُخْبِرُنا النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن صَرَفَ شيئًا مما يجب أن يكون لله إلى غيره، كدعاء غير الله تعالى، أو الاستغاثة بغيره، ومات على ذلك فإنه من أهل النار. وزاد ابن مسعود رضي الله عنه أن من مات وهو لا يشرك بالله شيًا فإنَّ مَصيرَه إلى الجنة.

  • الدعاء عبادةٌ لا يُصرف إلا لله تعالى.
  • فضل التوحيد، وأنَّ مَن مات عليه دخل الجنة، وإنْ عُذِّبَ على بعض ذنوبه.
  • خطر الشرك، وأنَّ مَن مات عليه دخل النار.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari