Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عن عبد الله بن مسعود قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «هَلَكَ الْمُتَنَطِّعُون» قالها ثلاثًا.
Fassara
Daga Abdullahi Dan Mas'ud ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Masu tsanantawa sun halaka" ya fadi hakan ne har sau uku.
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labari game da tabewar masu tsanantawa - ba tare da shiriya da ilimi ba - a addinin su da duniyar su, da kuma maganganun su da ayyuakan su, masu ketare iyakar shari'a da su wanda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi.
Fa'idoji
- Haramcin tsanantawa da dorawa kai abinda ba zai iyaba a cikin al'amura gaba dayan su, da kwadaitarwa akan nisantarhakan a kowane abu; musammanma a cikin ibadu da girmama salihai.
- Neman mafi cika a cikin ibadu da wasunsu al'amari ne abin yabo; kuma yana kasancewane ta hanyar bin shari'a.
- Son karfafa al'amari mai muhimmanci; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya maimaita wannan jumlar har sau uku.
- Martabar musulunci da kuma saukinsa.
Sharhi: العربية
يُخبرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن خَيْبَةِ وخَسارة المُتَشَدِّدين -على غير هدى وعلم- في دينِهم ودنياهم، وفي أقوالهم وأفعالهم، المتجاوزين بها الحدَّ الشرعيَّ الذي جاء به النبي صلى الله عليه وسلم.
- تحريم التشدُّد والتكلُّف في الأمور كلِّها، والحث على اجتنابه في كل شيء؛ لا سيَّما في العبادات وتعظيم الصالحين.
- طلب الأكمل في العبادة وغيرها أمر محمود؛ ويكون بمتابعة الشرع.
- استحباب تأكيد الأمر الهام؛ لأن النبي صلى الله عليه وسلم كرَّر هذه الجملة ثلاثًا.
- سماحة الإسلام ويُسْره.