Hadisai

Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «لَا يَقْبَلُ اللهُ صَلَاةَ أَحَدِكُمْ إِذَا أَحْدَثَ حَتَّى يَتَوَضَّأَ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala"

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa daga sharuddan ingancin sallah: Tsarki, to yana wajaba akan wanda ya yi nufin sallah ya yi alwala, in ya kasance wani abu mai warware alwala daga masu warware alwala ya faru agare shi; kamar bayan gida ko fitsari ko bacci ko wasunsu.

Fa'idoji

  • Sallar wanda ba shi da tsarki ba'a karbarta har sai ya yi tsarki, da yin wanka daga babban kari da kuma alwala daga karamin kari.
  • Alwala ita ce daukar ruwa da motsashi a baki da kuma fitar da shi, sannan jawo ruwa da numfashinsa zuwa cikin hancinsa, sannan fitar da shi da face shi, sannan wanke fuskarsa sau uku, sannan wanke hannayensa tare da gwiwoyin hannu sau uku, sannan shafar dukkanin kansa sau daya, sannan wanke kafafuwansa tare da idon sawu sau uku.
Sharhi: العربية

بَيّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مِن شروط صِحةِ الصلاةِ: الطهارةُ، فيَجبُ على مَن أرادَ الصلاةَ أنْ يتوضأ إنْ كان قد حصل منه ناقِضٌ من نواقض الوضوء؛ كالغائط أو البول أو النوم أو غيرِها.

  • صلاةُ المُحْدِثِ لا تُقبل حتى يتطهرَ بالغسل من الحَدَث الأكبر وبالوضوء من الأصغر.
  • الوضوء هو أَخْذُ ماءٍ وإدارته في الفم وإخراجه، ثم سحب الماء بنَفَسه إلى باطن أنفه، ثم إخراجه ونثره، ثم غسل وجهه ثلاث مرات، ثم غسل يديه مع المرفقين ثلاثًا، ثم مسح جميع رأسه مرة واحدة، ثم غسل رجليه مع الكعبين ثلاثًا.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari