Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عِمْرَانَ بْنِ حُصَيْنٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: السَّلَامُ عَلَيْكُمْ، فَرَدَّ عَلَيْهِ ثُمَّ جَلَسَ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «عَشْرٌ» ثُمَّ جَاءَ آخَرُ فَقَالَ: السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ، فَرَدَّ عَلَيْهِ فَجَلَسَ، فَقَالَ: «عِشْرُونَ» ثُمَّ جَاءَ آخَرُ فَقَالَ: السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ، فَرَدَّ عَلَيْهِ فَجَلَسَ، فَقَالَ: «ثَلَاثُونَ».
Fassara
Daga Imran ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum (Aminci ya tabbata agare ku), sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Goma» Sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Ashirin», sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Talatin».
Sharhi
Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum, (Aminci ya tabbata agare ku) sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: An rubuta masa lada goma, sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah, (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Yana da lada ashirin, sannan wani ya zo sai ya ce: (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Yana da lada talatin; wato kowane lafazi yana da lada goma.
Fa'idoji
- Mai zuw shi zai fara wa waɗanda ke zaune sallama.
- Karin lada (yana kasancewa ne) da ƙarin lafazan sallama.
- Mafi cika a yin sallama: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), kuma mafificiyar siga a amsa (sallama): Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Kuma aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa).
- Matakan sallama da amsawa masu wuce juna ne ladan ma haka.
- Koyawa mutane alheri da kuma faɗakar da su akan samun abinda ya fi.
- Ibnu Hajar ya ce: Da ace mai fara (sallama) zai ƙara (da rahamar Allah) an so a ƙara (da albarkarSa), da ace zai ƙara (da albarkarSa) shin a shara'anta ƙari a cikin amsawar? haka nan da ace mai fara (sallama) ya yi ƙari akan (da albarkarSa) shin an shara'anta masa hakan, (Imam) Malik ya fitar a cikin Muwaɗɗa daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Sallama tana ƙarewa ne zuwa albarka.
Sharhi: العربية
جاء رجل إلى النبي صلى الله عليه وسلم فقال: (السلام عليكم) فرد عليه ثم جلس، فقال النبي صلى الله عليه وسلم: كتب له عشر حسنات، ثم جاء آخر فقال: (السلام عليكم ورحمة الله)، فرد عليه فجلس، فقال النبي صلى الله عليه وسلم: له عشرون حسنة، ثم جاء آخر فقال: (السلام عليكم ورحمة الله وبركاته)، فرد عليه فجلس، فقال النبي صلى الله عليه وسلم: له ثلاثون حسنة؛ أي بكل لفظ عشر حسنات.
- القادم يبدأ الجالسين بالسلام.
- زيادة الأجر بزيادة ألفاظ السلام
- الأكمل في إلقاء السلام: (السلام عليكم ورحمة الله وبركاته)، وأفضل صيغة في الرد :(وعليكم السلام ورحمة الله وبركاته).
- مراتب السلام والرد متفاوتة والأجر متفاوت.
- تعليم الناس الخير وتنبيههم على تحصيل الأفضل.
- قال ابن حجر: لو زاد المبتدئ (ورحمة الله) استحب أن يزاد (وبركاته)، فلو زاد (وبركاته) فهل تشرع الزيادة في الرد؟ وكذا لو زاد المبتدئ على (وبركاته) هل يشرع له ذلك، أخرج مالك في الموطأ عن ابن عباس رضي الله عنهما قال: انتهى السلام إلى البركة.