Hadisai

Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ كَانَ يَقُولُ: «اللهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْهُدَى وَالتُّقَى، وَالْعَفَافَ وَالْغِنَى».

Fassara

Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: «Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata».

Sharhi

Ya kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Ya Allah ni ina roƙonKa shiriya» hanya madaidaiciya na sanin gaskiya da aiki da ita. «Da tsoron Allah», ruko da umarni da nisantar hane-hane. «Da kamewa» kamewa daga abinda ba ya halatta kuma ba shi da kyau na magana ne ko aiki. «Da wadatuwa» daga halitta, inda ba zai yi buƙatuwa ba zuwa ga wani inba Uabngijinsa - Mai girma da ɗaukaka ba -.

Fa'idoji

  • Ɗaukakar waɗannan ɗabi'un: Shiriya da tsoron Allah da kamewa da wadata, da kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da su.
  • Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya mallakawa kansa wani amfani ko cutarwa, wanda yake mallakar hakan Shi ne Allah - Maɗaukakin sarki -.
  • Wanda yake mallakar amfani da cutarwa da shiryar da halitta Shi ne Allah Shi kaɗai, ba wani mala'ika makusanci ba kuma ba wani Annabi abin aikowa ko waninsu ba.
Sharhi: العربية

كان من دعاء النبي صلى الله عليه وسلم: «اللهم إني أسألك الهدى» الطريق المستقيم من معرفة الحق والعمل به، «والتقى»، امتثال الأوامر واجتناب النواهي، «والعفاف» الكفّ عمّا لا يحل ولا يجمل من قول أو فعل، «والغنى» عن الخلق، بحيث لا يفتقر إلى أحد سوى ربِّه عز وجل.

  • شرف هذه الخصال: الهدى والتقى والعفاف والغنى، والحث على التخلق بها.
  • النبي صلى الله عليه وسلم لا يملك لنفسه نفعًا ولا ضرًّا، وأن الذي يملك ذلك هو الله تعالى.
  • الذي يملك النفع والضر والهداية للخلق هو الله وحده، لا ملك مُقرّب ولا نبي مرسل ولا غيرهما.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari