Hadisai

Ka shiryar da ni ga wani aiki wanda idan na yi shi, zan shiga aljanna, ya ce: "Ka bauta wa Allah, kada ka hada Shi da komai, ka tsayar da sallah, ka bayar da zakkar da aka wajabta, ka azimci Ramadan

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ أَعْرَابِيًّا أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: دُلَّنِي عَلَى عَمَلٍ إِذَا عَمِلْتُهُ دَخَلْتُ الجَنَّةَ، قَالَ: «تَعْبُدُ اللَّهَ لاَ تُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا، وَتُقِيمُ الصَّلاَةَ المَكْتُوبَةَ، وَتُؤَدِّي الزَّكَاةَ المَفْرُوضَةَ، وَتَصُومُ رَمَضَانَ» قَالَ: وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ لاَ أَزِيدُ عَلَى هَذَا، فَلَمَّا وَلَّى قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ سَرَّهُ أَنْ يَنْظُرَ إِلَى رَجُلٍ مِنْ أَهْلِ الجَنَّةِ، فَلْيَنْظُرْ إِلَى هَذَا».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Cewa wani balaraben kauye ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ka shiryar da ni ga wani aiki wanda idan na yi shi, zan shiga aljanna, ya ce: "Ka bauta wa Allah, kada ka hada Shi da komai, ka tsayar da sallah, ka bayar da zakkar da aka wajabta, ka azimci Ramadan" Ya ce: Na rantse da Wanda raina yake a hannunSa, ba zan yi kari akan wannan ba, lokacin da ya juya ya tafi sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda yake son ya kalli wani mutum daga 'yan aljanna, to ya yi duba zuwa ga wannan".

Sharhi

Wani mutum ya gabato daga mutanen kauye ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan ya nuna masa aikin da zai shigar da shi aljanna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa da cewa shiga aljanna da tsira daga wuta sun tsaya akan bada rukunan Musulunci, na bautar Allah Shi kadai, kuma kada ka hada wani abu da Shi. Ka tsaida salloli biyar din Allah Ya wajabta su akan bayinSa a kowanne yini da dare. Ka bada zakkar dukiyar da Allah Ya wajabtasu akanka, ka bada su ga wadanda suka cancanta l. Ka kuma kiyaye akan azimin watan Ramadan a lokacinsa. Sai mutumin ya ce na rantse da wanda raina yake a hannunSa ba zan kara komai akan aikin da aka wajabta ba wanda na ji shi daga gareka na ayyukan da'a ba, kuma ba zan rage ba daga garesu ba. Lokacin da ya juya (ya tafi) sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Wanda yake son ya yi duba zuwa ga wani mutum daga 'yan aljanna to ya yi duba zuwa ga wannan balaraben kauyen.

Fa'idoji

  • Kadaita Allah - Madaukakin sarki - da ibada shi ne farkon abinda ake farawa da shi a kira zuwa ga Allah.
  • Takaituwa da koyar da wajibai ga wanda ya zama farkon shiga Musulunci.
  • Kira zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - babu makawa daga bi a sannu a sannu.
  • Kwadayin mutumin akan neman sanin al'amarin Addininsa
  • Idan musulmi ya takaita akan wajibai to cewa shi ya tsira, saidai anan ba ya nufin sakaci ga nafilifili; domin nafila ana cike tawayar farilla da ita.
  • Kebance wasu daga ibadu da ambato dalili ne akan muhimmancinsu da kwadaitarwa akan su, (hakan) ba ya nufin rashin wajabcin waninta.
Sharhi: العربية

قَدِمَ رجلٌ مِن أهلِ الباديةِ على النبيِّ صلى الله عليه وسلم لِيَدُلَّه على عَملٍ يُدخله الجنة، فأجابه النبي صلى الله عليه وسلم بأنَّ دخول الجنة والنجاة من النار يَتَوَقَّفانِ على أداء أركان الإسلام، من عبادة الله وحده، وأن لا تشرك به شيئًا. وتقيم الصلوات الخمس التي أوجبها الله على عباده في كل يوم وليلة. وتعطي زكاة المال التي أوجبها الله عليك، وتدفعها لمستحقها. وتحافظ على صيام شهر رمضان في وقته. قال الرجل والذي نفسي بيده لا أزيد على العمل المفروض الذي سمعته منك شيئًا من الطاعات، ولا أنقص منه. فلما انصرف قال النبي صلى الله عليه وسلم: مَن سرَّه أن يَنظرَ إلى رجل من أهل الجنة فلينظر إلى هذا الأعرابي.

  • توحيد الله تعالى بالعبادة أول ما يُبدأ به في الدعوة إلى الله.
  • الاكتفاء بتعليم الواجبات على مَن كان حديثَ عهدٍ بإسلام.
  • الدعوة إلى الله تعالى لا بُد فيها من التدرُّج.
  • حرص الرجل على تَعلُّم أمر دينه.
  • إذا اقتصر المسلم على الواجبات فإنه يفلح، ولكن لا يعني هذا التساهل بالتطوعات؛ لأن التطوع يُكمل به النقص بالفرائض.
  • تخصيص بعض العبادات بالذكر دليل على أهميتها والحض عليها، ولا يعني عدم وجوب غيرها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari