Hadisai

An kewaye wuta da sha'awowi, kuma an kewaye Aljanna da abubuwa ki

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «حُجِبَتِ النَّارُ بِالشَّهَوَاتِ، وَحُجِبَتِ الْجَنَّةُ بِالْمَكَارِهِ».

Fassara

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "An kewaye wuta da sha'awowi, kuma an kewaye Aljanna da abubuwa ki".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wuta abar kewayewace da al'amuran da rai take son sha'awrsu na aikata abubuwan da aka haramta, ko takaitawa a wajibai; Duk wanda ya bi son ransa a hakan to ya cancanci wuta, Kuma cewa Aljanna abar kewayewace da al'amuran da rai take kin su; kamar lazimta akan abubuwan da aka umarta da barin abubuwan da aka haramta, da hakuri akan hakan, idan ya kutsa kuma ya yaki ransa a hakan to ya cancanci shiga Aljanna.

Fa'idoji

  • Daga sabubban afkawa a sha'awowi kawatawar Shaidan abin ki da mummuna, har rai ya gan shi mai kyau ne, sai ya karkata zuwa gare shi.
  • Umarni da nisantar sha'awowin da aka haramta; domin cewa su hanya ce zuwa wuta, da kuma hakuri akan abubuwan ki; domin cewa su hanya ce ta zuwa Aljanna.
  • Falalar yakar rai ko kokari a ibada, da kuma hakuri akan abubuwan ki da wahalar da ke kewaye ayyukan biyayya.
Sharhi: العربية

يُبيِّنُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ النارَ مَحفوفةٌ مُحاطةٌ بالأمور التي تَشتَهيها النفس مِن فِعْل المحرّمات أو التقصير في الواجبات، فمن أَتْبعَ نفسَه هواها في ذلك استحقَّ النار. وأنَّ الجنةَ محفوفةٌ محاطةٌ بالأمور التي تَكرهها النفس؛ كالمُواظَبةِ على المأمورات وترك المحرمات والصبر على ذلك، فإذا صبر وجاهد نفسه على فعل الطاعة وترك المعصية؛ دخل الجنة.

  • من أسباب الوقوع في الشهوات تزيينُ الشيطانِ المنكرَ والقبيحَ، حتى تراه النفس حسنًا فتَميلُ إليه.
  • الأمر بالابتعاد عن الشهوات المحرمة؛ لأنها الطريق إلى النار، والصبر على المكاره؛ لأنها الطريق إلى الجنة.
  • فضل مجاهدة النفس والاجتهاد في العبادة والصبر على المكاره والمشاق التي تحيط بالطاعات.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari