Hadisai

An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har saida ya wayi gari a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: "Wancan wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnuwansa, ko ce ya yi: A cikin kunnensa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ مسعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: ذُكِرَ عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلٌ نَامَ لَيْلَهُ حَتَّى أَصْبَحَ، قَالَ: «ذَاكَ رَجُلٌ بَالَ الشَّيْطَانُ فِي أُذُنَيْهِ، أَوْ قَالَ: فِي أُذُنِهِ».

Fassara

Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har saida ya wayi gari a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: "Wancan wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnuwansa, ko ce ya yi: A cikin kunnensa".

Sharhi

An anbaci wani mutumin da ya yi bacci har gari ya waye rana ta ɓullo bai tashi ya yi sallar farilla ba a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai shi wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnansa.

Fa'idoji

  • Karhancin barin tsayuwar dare, kuma cewa hakan da sababin Shaiɗan ne.
  • Tsoratarwa daga Shaiɗan wanda yake zama ga mutum a kan kowace hanya; dan ya tsare tsakaninsa da tsakanin ɗa'ar Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
  • Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa: (Bai tashi zuwa sallah ba) abin nufi jinsi, kuma zai iya ɗaukar alƙawari, kuma ana nufin sallar dare ko (sallar) farillah da shi.
  • Al-Ɗaibi ya ce: An keɓanci kunne da anbato, duk da ido yafi dacewa da bacci, dan yin nuni zuwa nauyin bacci, domin cewa kunnuwa sune magangarar farkawa, kuma an keɓanci fitsari; domin cewa shi ya fi sauƙin shiga a cikin ciki, kuma mafi saurin zarcewa a cikin jijiyoyi, sai ya gadar da kasala a cikin dukkan gaɓɓai.
Sharhi: العربية

ذُكِرَ عند النبيِّ صلى الله عليه وسلم رَجلٌ نام حتى أصبح وطَلَعت الشمس ولم يَقم إلى الصلاة المفروضة، فقال صلى الله عليه وسلم: إنه رجل بَالَ الشيطانُ في أُذُنِهِ.

  • كراهية ترك قيام الليل، وأنّ ذلك بسبب الشيطان.
  • الحَذَر من الشيطان الذي يَقعد للإنسان في كل طريق؛ لِيَحُوْلَ بينه وبين طاعة الله عز وجل.
  • قال ابن حجر: قوله: (ما قام إلى الصلاة) المُراد الجِنْس، ويحتمل العهد، ويراد به صلاة الليل أو المكتوبة.
  • قال الطيبي: خص الأذن بالذِّكْر، وإن كانت العين أنسب بالنوم إشارة إلى ثقل النوم، فإن المسامع هي موارد الانتباه، وخص البول؛ لأنه أسهل مدخلًا في التجاويف، وأسرع نفوذًا في العروق، فيورث الكسل في جميع الأعضاء.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari