Hadisai

Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لَا يَسْتُرُ عَبْدٌ عَبْدًا فِي الدُّنْيَا إِلَّا سَتَرَهُ اللهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wani musulmi ba zai suturta ɗan uwansa musulmi ba a cikin wani al'amari daga al'amura, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya suturta shi a ranar alƙiyama; sakayya tana daga jinsin aiki, kuma suturcewar Allah gare shi zai zama da suturcewar laifukansa da saɓonsa daga yaɗasu ga ma'abota taron alƙiyama, zai iya kasancewa da barin yi masa hisabi akansu da kuma anbata masa su.

Fa'idoji

  • Halaccin rufawa musulmi asiri idan ya aikata wani saɓo, tare da yin inkari akansa da kuma yi masa nasiha, da tsoratar da shi Allah, amma idan ya kasance daga ma'abota sharri da ɓarna ne masu bayyana saɓo da fasiƙanci, to cewa shi ba ya kamata a rufa musu asiri; domin rufa musu asiri zai sa su ƙarfin hali akan saɓo, kawai ana ɗaga al'amarinsa ne zuwa ga hukuma, koda a hakan akwai anbatansa; domin cewa shi mai bayyanar da fasiƙancinsa ne da kuma saɓonsa.
  • Kwaɗaitarwa a kan rufa asirin kurakuren wasu.
  • Daga fa'idojin rufa asiri: Bada dama ga mai yin zunubi ya yi tinani kuma ya tuba zuwa ga Allah; domin bayyanar da aibuka da al'aurori yana daga yayata alfasha, kuma yana ɓata yanayin zamantakewa, kuma yana ruɗar mutane da aikata su.
Sharhi: العربية

يُبَيِّنُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنه لا يَستر مسلمٌ أخاه المسلم في أمر من الأمور، إلا سَتره الله عز وجل يوم القيامة؛ فالجزاء من جنس العمل، ويكون سِتْرُ اللهِ له بستر عيوبه ومعاصيه عن إذاعتها على أهل المحشر، وقد يكون بترك محاسبته عليها وذكرها له.

  • مشروعية السِّتْر على المسلم إذا فَعَلَ معصية، مع الإنكار عليه، والنصيحة له، وتخويفه بالله، أما إذا كان من أهل الشر والفساد المجاهرين بالمعاصي والفسق، فإنه لا ينبغي الستر عليهم؛ لأن الستر عليهم يُجَرِّئُهم على المعاصي، وإنما يُرْفَع أمرُه إلى ولاة الأمور، ولو كان في هذا ذكر له؛ لأنه مُعْلِن بفسقه ومعصيته.
  • الترغيب في ستر أخطاء الآخرين.
  • من فوائد الستر: إتاحة الفرصة للمذنب أن يراجِعَ نفسه ويتوب إلى الله؛ لأن إعلان العيوب والعورات من إشاعة الفاحشة، ويُفسِد الجَوَّ الاجتماعي، ويُغْرِي الناس بارتكابها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari