Hadisai

Ka guji duniya sai Allah Ya so ka, ka guji abin da ke hannun mutane sai mutane su so ka

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Nawawi ya ce: Hadisi ne mai kyauIbnu Majah da waninsa ne suka ruwaito shi da isnadai kyakkyawa

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي العَبَّاسِ سَهْلِ بْنِ سَعِدٍ السَّاعِدِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، دُلَّنِي عَلَى عَمَلٍ إِذَا عَمِلْتُهُ أَحَبَّنِي اللَّهُ وَأَحَبَّنِي النَّاسُ، فَقَالَ: «ازْهَدْ فِي الدُّنْيَا يُحِبُّكَ اللَّهُ، وَازْهَدْ فِيمَا عِنْدَ النَّاسِ يُحِبُّكَ النَّاسُ».

Fassara

Daga Abul Abbas Sahlu ibnu Sa'ad al-Sa'idi - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, ka shiryar da ni akan aikin da idan na aikata shi Allah zai soni mutane ma za su so ni, sai ya ce: «Ka guji duniya sai Allah Ya so ka, ka guji abin da ke hannun mutane sai mutane su so ka».

Sharhi

Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da shi zuwa aikin da idan ya aikata shi Allah zai so shi kuma mutane ma zasu so shi, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Allah zai so ka idan ka bar mafifici a duniya, da abin da ba zai amfaneka a lahira ba, kuma ka bar abin da zai iya yi wuwa a cikinsa akwai cutarwa a Addinika, kuma mutane zasu so ka idan ka guji abinda ke hannunsu na duniya; domin su a ɗabi'arsu suna sonta, wanda kuwa ya yi gogayya da su a kanta zasuƙi shi, wanda ya bar musu ita zasu so shi.

Fa'idoji

  • Falalar gujewa duniya, shi ne: Yabar abin da ba zai amfanar a lahira ba.
  • Gudun duniya darajarsa ta fi tsantseni; domin cewa tsantseni shi ne barin abin da zai iya cutarwa, gudun duniya kuwa shi ne barin abin da ba zai amfanar a lahira ba.
  • Sindi ya ce: Lallai cewa duniya abar so ce a wurin mutane, duk wanda ya yi gogayya da su a cikinta zai zama abin ƙi a wurinsu gwargwadan haka, wanda kuma ya barsu da abar sonsu zai zama abin so a cikin zukatansu gwargwadan hakan.
Sharhi: العربية

سَأل رجل النبي صلى الله عليه وسلم أن يرشده إلى عمل إذا عمله أحبه الله وأحبه الناس، فقال له صلى الله عليه وسلم: يحبك الله إذا تركت الفاضل من الدنيا، وما لا ينفعك في الآخرة، وتركت ما قد يكون فيه ضرر في دينك، ويحبك الناس إذا زهدت بما في أيديهم من الدنيا؛ لأنهم يحبونها بطبعهم، ومن زاحمهم عليها أبغضوه، ومن تركها لهم أحبوه.

  • فضيلة الزهد في الدنيا، وهو: أن يترك ما لا ينفع في الآخرة.
  • الزهد مرتبته أعلى من الورع؛ لأن الورع ترك ما قد يضر، والزهد ترك ما لا ينفع في الآخرة.
  • قال السندي: إن الدنيا محبوبة عند الناس فمن يزاحمهم فيها يصير مبغوضًا عندهم بقدر ذلك، ومن تركهم ومحبوبهم يكون محبوبًا في قلوبهم بقدر ذلك.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari