Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي مُوسَى رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ يَبْسُطُ يَدَهُ بِاللَّيْلِ لِيَتُوبَ مُسِيءُ النَّهَارِ، وَيَبْسُطُ يَدَهُ بِالنَّهَارِ لِيَتُوبَ مُسِيءُ اللَّيْلِ، حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ مِنْ مَغْرِبِهَا».
Fassara
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lalle ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yana shimfiɗa hannunSa da daddare domin mai laifi da rana ya tuba, kuma Yana shimfiɗa hannunSa da rana domin mai laifi da daddare ya tuba, har sai rana ta ɓullo daga yammacinta".
Sharhi
Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Allah - Maɗaukakin sarki - Yana karɓar tuba daga bayinSa. Idan bawa ya yi laifi da rana kuma ya tuba da daddare Allah Zai karbi tubansa, idan ya yi laifi da daddare ya kuma tuba da rana Allah Zai karɓi tubansa. Kuma tsarki ya tabbatar maSa Yana shinfiɗa hannunSa dan tuba dan farin ciki da tuban, da kuma karɓar tuban, ƙofar tuba tana nan a bude har sai rana ta ɓullo daga yammacinta dan alamtar wa da ƙarewar duniya, idan ta ɓullo to za'a kulle ƙofar tuba.
Fa'idoji
- Karɓar tuba yana nan muddin ƙofar na nan a buɗe, kuma ana kulle ƙofarta ne da ɓullowar rana daga mafaɗarta. Kuma idan mutum ya tuba kafin gargarar mutuwa, shi ne rai ya kai maƙogwaro.
- Rashin yanke ƙauna saboda zunubi, domin cewa afuwar Allah - tsarki ya tabbatar maSa - da rahamarSa masu yalwa ne, kuma ƙofar tuba abuɗe take.
- Sharuɗɗan tuba: Na ɗaya: Barin aikata laifin. Na biyu: Nadama akan aikata shi. Na uku: Kudirce niyya akan ba zai koma zuwa gare shi ba har abada. Wannan idan ya kasance a cikin haƙƙoƙin Allah - Maɗaukakin sarki - ne, idan ya kasance ya rataya da haƙƙin wani daga haƙƙoƙin bayi, to an sharɗanta ga ingancin tuban ya mayar da wannan haƙƙin ga mai shi, ko mai haƙƙin ya yi masa afuwa.
Sharhi: العربية
يُخبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم: أنَّ الله تعالى يقبل التوبة من عباده، فإن أذنب العبد ذنبًا بالنهار وتاب بالليل قَبِلَ الله توبته، وإن أذنب ذنبًا بالليل وتاب بالنهار قَبل الله توبته، ويبسط يده سبحانه للتوبة فرحًا بها، وقبولًا لها، ولا يزال باب التوبة مفتوحًا حتى تطلع الشمس من مغربها إيذانًا بانتهاء الدنيا، فإذا طلعت فإن باب التوبة يُغلق.
- قبول التوبة مستمر ما دام بابها مفتوحًا، ويغلق بابها بمطلع الشمس من مغربها، وأن يتوب الإنسان قبل غرغرة الموت، وهي وصول الروح إلى الحلقوم.
- عدم اليأس والقنوط بسبب الذنب، فإن عفو الله سبحانه ورحمته واسعة، وباب التوبة مفتوح.
- شروط التوبة: الأول: الإقلاع عن المعصية، والثاني: الندم على فعلها، والثالث: العزم على ألّا يعود إليها أبدًا، هذا إن كانت في حقوق الله تعالى، وإن كانت متعلِّقة بحق من حقوق العباد، فيشترط لصحة التوبة أن يؤدي ذلك الحق إلى صاحبه، أو يعفو عنه صاحب الحق.