Hadisai

Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikinmu, daga kowane ƙaramin (yaro) da babba, ɗa ne ko bawa, Sa’i na abinci, ko Sa’i na cukwi, ko Sa’i na sha'ir, ko Sa’i na dabino, ko Sa’i na zabibi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: كُنَّا نُخْرِجُ إِذْ كَانَ فِينَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الْفِطْرِ، عَنْ كُلِّ صَغِيرٍ وَكَبِيرٍ، حُرٍّ أَوْ مَمْلُوكٍ، صَاعًا مِنْ طَعَامٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ أَقِطٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ زَبِيبٍ، فَلَمْ نَزَلْ نُخْرِجُهُ حَتَّى قَدِمَ عَلَيْنَا مُعَاوِيَةُ بْنُ أَبِي سُفْيَانَ رضي الله عنه حَاجًّا، أَوْ مُعْتَمِرًا فَكَلَّمَ النَّاسَ عَلَى الْمِنْبَرِ، فَكَانَ فِيمَا كَلَّمَ بِهِ النَّاسَ أَنْ قَالَ: إِنِّي أَرَى أَنَّ مُدَّيْنِ مِنْ سَمْرَاءِ الشَّامِ، تَعْدِلُ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، فَأَخَذَ النَّاسُ بِذَلِكَ، قَالَ أَبُو سَعِيدٍ: فَأَمَّا أَنَا فَلَا أَزَالُ أُخْرِجُهُ كَمَا كُنْتُ أُخْرِجُهُ، أَبَدًا مَا عِشْتُ.

Fassara

Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikinmu, daga kowane ƙaramin (yaro) da babba, ɗa ne ko bawa, Sa’i na abinci, ko Sa’i na cukwi, ko Sa’i na sha'ir, ko Sa’i na dabino, ko Sa’i na zabibi, kuma bamu gushe ba muna fitar da shi har saida Mu'awiya ɗan Abu Sufyan - Allah Ya yarda da shi - ya gabato gurinmu yana mai aikin Hajji, ko yana mai Umarah sai ya yi wa mutane magana akan minbari, ya kasance daga abinda ya yi wa mutane magana da shi cewa ya ce: Lallai ni na ga cewa mudu biyu na alkamar Sham, sun yi daidai da sa'i ɗaya na dabino, sai mutane suka yi riko da hakan, Abu sa'id ya ce: Ammma ni ba zan gushe ba ina fitar da shi kamar yadda na kasance ina fitar da shi, muddin dai na rayu har abada.

Sharhi

Musulmai sun kasance suna fitar da zakkar fidda kai Sa’i ɗaya na abinci a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da zamanin Khalifofi masu shiryarwa a bayansa daga ƙaramin (yaro) da babba. Abin cin su ya kasance sha'ir ne da (zabibi): Bushasshen inibi, da (cukwi): Busasshen nono da kuma dabino. Gwargwadan Sa’i mudu huɗu ne, mudu kuma ya yi daidai da cikin tafi biyu na namiji madaidaici (ba babba ba ba kuma ƙarami ba). Lokacin da Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya zo Madina alhali shi yana Khalifa, kuma alkamar Sham ta yi yawa, sai ya yi huɗuba sai ya ce: Lallai ni ina ganin cewa mudu biyu na alkamar Sham (rabin Sa’i), sun yi daidai da Sa’i ɗaya na dabino, sai mutane suka yi riƙo da hakan. Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Amma ni ba zan gushe ba ina fitar da shi kamar yadda na kasance ina fitar da shi a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi har abada muddin dai ina raye.

Fa'idoji

  • Bayanin gwargwadan sadakar fidda kai a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Sa’i ne na abinci koda jinsi da ƙima sun saɓa.
  • Dukkan abin cin 'yan Adam mai isuwa ne a (zakkar) fidda kai, kawai an keɓanci nau'ikan nan huɗu da ambato ne; domin cewa sune abincin mutane a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Fitar da wanin abinci na sulalla da kuɗi, ba ya isuwa a (zakkar) fidda kai.
  • AlNawawi ya faɗa a a Sharhin Muslim: Idan sahabbai suka saɓa to maganar sashinsu ba ta zama mafi cancanta daga sashi ba, sai mu koma zuwa ga wani dalilin daban, mun samu cewa zahirin hadisan da ƙiyasin sun haɗu a kan sharɗanta kwano na alkama kamar waninta, sai dogaro a kansa ya wajaba.
  • Ibnu Hajar ya ce: A cikin hadisin Abu Sa'id akwai abinda ya kasance akansa na tsananin biyayya da riƙo da tafarkin magabata, da barin bauɗewa zuwa ijtihadi tare da samun nassi, kuma a cikin aikin Mu'awiya da amsawar mutane gare shi akwai nuni akan halaccin ijtihadi, kuma shi abin so ne, saidai ijtihadi tare da samuwar nassi to (zai zama) mai ɓataccen lura.
Sharhi: العربية

كَانَ المسلمون يُخْرِجون زكاةَ الفطر في عهد النبي صلى الله عليه وسلم وعهد الخلفاء الراشدين مِن بعده عن الصغير والكبير مِقدار صاعٍ من طعام. وكان طعامهم الشعير و(الزبيب): العنب اليابس، و(الأقط): اللبَن المُجَفَّف والتمر. ومقدار الصاع أربعة أَمْداد، والمُدُّ يساوي مِلءَ كَفَّي الرجل المعتدل. فلما جاء معاوية رضي الله عنه للمدينة وهو خليفة، وكَثُر القَمْح الشامي، خطب فقال: إني أرى أن مُدَّين من قمح الشام (نصف صاع)، تَعْدِل صاعًا من التمر، فأخذ الناس بذلك. قال أبو سعيد الخدري رضي الله عنه: فأما أنا فلا أَزال أُخْرِجه كما كنت أُخْرِجه في عهد النبي صلى الله عليه وسلم أبدًا ما عشت.

  • بيان مقدار صدقة الفطر في زمن النبي صلى الله عليه وسلم، صاع من طعام وإن اختلف الجنس والقيمة.
  • كل طعام للآدميِّين مجزئ في الفِطْرَة، وإنما خُصَّت الأصناف الأربعة بالذِّكْر؛ لأنها كانت طعام الناس في عهد النبي صلى الله عليه وسلم.
  • إخراج غير الطعام من الفلوس والنقود، لا يجزئ في الفطرة.
  • قال النووي على شرح مسلم: وإذا اختلفت الصحابة لم يكن قولُ بعضِهم بأولى من بعض، فنرجع إلى دليل آخر، وجدنا ظاهر الأحاديث والقياس متفقًا على اشتراط الصاع من الحِنْطة كغيرها، فوجب اعتماده.
  • قال ابن حجر: وفي حديث أبي سعيد ما كان عليه من شدة الاتباع والتمسك بالآثار، وترك العدول إلى الاجتهاد مع وجود النص، وفي صنيع معاوية وموافقة الناس له دلالة على جواز الاجتهاد، وهو محمود، لكنه مع وجود النص فاسدُ الاعتبار.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari