Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَرَأَى زِحَامًا وَرَجُلًا قَدْ ظُلِّلَ عَلَيْهِ، فَقَالَ: «مَا هَذَا؟»، فَقَالُوا: صَائِمٌ، فَقَالَ: «لَيْسَ مِنَ البِرِّ الصَّوْمُ فِي السَّفَرِ»، وَفِي لَفْظٍ لِمُسلِمٍ: «عَلَيْكُمْ بِرُخْصَةِ اللهِ الَّذِي رَخَّصَ لَكُمْ».
Fassara
Daga Jabir ɗan Abdullah -Allah Ya yarda da su -, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a wata tafiya, sai ya ga cunkoso da wani mutum an yi masa inuwa, sai ya ce: «Menene wannan», sai suka ce: Mai azimi ne, sai ya ce: «Azimi a halin tafiya bai zama daga aikin alheri ba». A cikin wani lafazin na Muslim: «Na horeku da rangwamin da Allah Ya yi muku».
Sharhi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin wata tafiya, sai ya ga wani mutum mutane sun haɗu a kansa alhali an yi masa inuwa saboda zafin rana da tsananin ƙishirwa, sai ya ce: Me ya same shi ? sai suka ce: Mai azimi ne, sai ya ce: Azimi a halin tafiya bai zama daga cikin ayyukan alheri ba, na horeku da rangwamin da Allah Yayi muku.
Fa'idoji
- Bayanin sauƙin shari'ar Musulunci.
- Halaccin yin Azumi a halin tafiya, da kuma halaccin riƙo da rangwami da barin yin azimin.
- An hana yin azumi a halin tafiya idan azumin yana yi masa wahala, muddin dai bai kai iyakar mutuwa ba sai (azimin) ya haramta.
- Nawawi ya ce: Ba aikin alheri ba ne ku yi azimi a halin tafiya: ma'anarsa: Idan azumin yana yi muku wahala, kuma kuka ji tsoron cuta, siyaƙin hadisin yana hukunta wannan tawilin.
- Kulawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sahabbansa da yadda yake tambayar halayensu.
Sharhi: العربية
كان رسول الله صلى الله عليه وسلم في سفر، فرأى رجلًا اجتمع الناس عليه وقد ظُلِّل عليه من حرارة الشمس وكثرة العطش، فقال: ما له؟ فقالوا: صائم، فقال: ليس من البر الصوم في السفر، عليكم برخصة الله الذي رخص لكم.
- بيان يُسْر شريعة الإسلام.
- جواز الصيام في السفر، وجواز الأخذ بِالرُّخْصَةِ بالفطر.
- يكره الصوم في السفر إذا شق عليه، ما لم يصل به إلى حدِّ الهَلكة فيَحْرُم.
- قال النووي: ليس من البر أن تصوموا في السفر: معناه: إذا شق عليكم وخفتم الضرر، وسياق الحديث يقتضي هذا التأويل.
- اعتناء النبي صلى الله عليه وسلم بأصحابه وسؤاله عن أحوالهم.