Hadisai

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الفِطْرِ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ، عَلَى العَبْدِ وَالحُرِّ، وَالذَّكَرِ وَالأُنْثَى، وَالصَّغِيرِ وَالكَبِيرِ مِنَ المُسْلِمِينَ، وَأَمَرَ بِهَا أَنْ تُؤَدَّى قَبْلَ خُرُوجِ النَّاسِ إِلَى الصَّلاَةِ.

Fassara

Daga Ɗan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai bayan (azimin) Ramadan, ita gwargwadan Sa'i ne (wanda) awonsa yakai mudun Nabiyyi huɗu. Mudun Nabiyyi: (Shi ne) cikin tafukan mutum madaidaici, na dabino ko alkama akan kowane musulmi; ɗa da bawa, namiji da mace, ƙarami da babba, hakan ga wanda a wajensa akwai abinda ya rage daga abin cin yininsa da darensa, (zai fitarwa) kansa da kuma wanda yake kula da su. Kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi.

Fa'idoji

  • Zakkar fidda kai ta azimi tana wajaba a fitar wa yaro ita da babba, da ɗa da bawa, kuma ana yi wa waliyyin (yaro) da mamallakin (bawa) umarni da ita, kuma mutum yana fitarwa kansa da 'ya'yansa da wanda ciyarwarsu take wajaba akansa.
  • Zakkar fidda kai ba ta wajaba daga ɗan tayi, saidai an so (a fitar masa).
  • Bayanin abinda ake fitarwa a zakkar fidda kai, shi ne abincin mutane na al'ada.
  • Wajabcin fidda ita kafin sallar idi, abinda ya fi ta kasance a safiyar idi, kuma fitar da ita yana halatta kafin idi da kwana ɗaya ko kwanaki biyu.
Sharhi: العربية

أَوْجَبَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم زكاةَ الفطر بعد رمضان، وهي بمِقْدار صاعٍ يَبلغ وزنه أربعة أمداد. والمُدُّ: مِلْء كَفَّي الرجُل المتوسّط، مِن تمر أو شعير على كل مسلم؛ الحر والعبد، الذكر والأنثى، الصغير والكبير، وذلك لمن عنده ما يَفيض عن قوت يومه وليلته، عن نفسه وعمّن يَعولهم. وأَمَرَ أن تُؤدّى قبل خروج الناس إلى صلاة العيد.

  • زكاة الفطر مِن رمضان يجب أن تُؤدّى عن الصغير والكبير، والحر والمملوك، ويُخاطَب بها الوليّ والسِّيِّد، ويُخْرِجُها الرَّجل عنه وعن أولاده ومَن تَجِب عليه نَفَقتُهم.
  • لا تجب زكاة الفطر عن الجَنين، بل تُستحب.
  • بيان ما يُخرَج في زكاة الفطر، وأنه قوت الناس المعتاد.
  • وجوب إخراجها قبل صلاة العيد، والأفضل أن تكون في صباح العيد، ويجوز إخراجها قبل العيد بيوم أو يومين.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari