Hadisai

Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «تَحَرَّوْا لَيْلَةَ القَدْرِ فِي الوِتْرِ مِنَ العَشْرِ الأَوَاخِرِ مِنْ رَمَضَانَ».

Fassara

Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan yin ƙoƙari a nema da kirdadon daren lailatul-ƙadr da yawaita aiki na gari, shi ne mafi ƙauna ya kasance a darare na mara daga goman ƙarshe a Ramadan a kowace shekara, sune: Ashirin da ɗaya, da ashirin da uku, da ashirin da biyar, da ashirin da bakwai, da ashirin da tara.

Fa'idoji

  • Falalar lailatul-ƙadr da kwaɗaitarwa akan kirdadonsa.
  • Daga hikimar Allah da rahamarSa cewa Ya ɓoye wannan daren dan mutane su yi ƙoƙari a cikin ibada, dan neman sa, sai ladansu ya yi yawa.
  • Daren Lailatul-ƙadr a goman ƙarshe na Ramadan (yake), kuma an fi ƙauna a mara daga gare shi .
  • Daren Lailatul-ƙadr ɗaya ne daga dararen goman ƙarshe na Ramadan, shi ne daren da Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da Al-Kur'ani a cikinsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma Ya sanya wannan daren ya fi wata dubu a albarkarsu, da girman darajarsu, da tasirin aiki na gari a cikinsu.
  • An ambaci (Lailatul-ƙadr) da yi wa (Dal ) ɗauri da hakan, kodai daga ɗaukaka ne, sai ace: Wane mai girman daraja ne, sai raɓawar daren ta zama daga babin raɓawar abu zuwa siffarsa, wato dare maɗaukaki, yana nufin cewa shi mai girman daraja ne da ɗaukaka da buwaya da matsayi zuwa ƙarshensa, (lallai Mu Mun saukar da shi a cikin wani dare Mai albarka). [al-Dukhan: 3], ko kuma daga ƙaddarawa ne: Sai raɓawar gare shi ta zama daga raɓawar Zarfi zuwa abinda yake tattaroshi, wato wannan daren wanda a cikinsa akwai ƙaddarawar abinda yake gudana a cikin shekara, (A cikinta ne ake rarraba kowane al'amarin da ake hukuntawa) [al-Dukhan: 4].
Sharhi: العربية

حَثَّ النبيُّ صلى الله عليه وسلم على الاجتهاد في التماس وتَحرِّي وطلب ليلة القدر بالإكثار من العمل الصالح، وهي أرجى أن تكون في الليالي الوترية من العشر الأواخر من رمضان كل عام، وهي: الحادية والعشرون، والثالثة والعشرون، والخامسة والعشرون، والسابعة والعشرون، والتاسعة والعشرون.

  • فضل ليلة القَدْر والحثّ على تَحَرِّيها.
  • من حكمة الله ورحمته أخفى هذه الليلة لِيَجِدَّ الناس في العبادة، طلبًا لها، فيَكثُر ثوابُهم.
  • ليلة القَدْر في العشر الأواخر من رمضان، وفي الأوتار منه أرجى.
  • ليلة القدر هي إحدى ليالي العشر الأواخر من رمضان، وهي الليلة التي أنزل الله عز وجل فيها القرآن على النبي صلى الله عليه وسلم، وجعل هذه الليلة خيرًا من ألف شهر في بركتها، وعظيم قدرها، وأثر العمل الصالح فيها.
  • سميت (ليلة القدْر) بسكون الدال بذلك، إما من الشرف، فيُقال: فلان عظيم القدر، فتكون إضافة الليلة من باب إضافة الشيء إلى صفته، أي الليلة الشريفة، يعني أنها عظيمة القدر شرفًا وفخامة ومكانة إلى آخره، ﴿ إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُبَارَكَةٍ ﴾ [الدخان: 3]، وإما من التقدير: فتكون إضافتها إليه من إضافة الظرف إلى ما يحتويه، أي هذه الليلة التي يكون فيها تقدير ما يجري في السنة، ﴿ فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ ﴾ [الدخان: 4].

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari