Hadisai
GOMAN ƘARSHE TA RAMADAN
Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
sakamako 6
- 3755
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ƙoƙari a cikin goman ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a cikin waninsa
Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi - 4202
Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa
Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi - 4459
Duk wanda ya yi E'itikafi tare da ni to yayi a goman karshe domin nagani a wannan daren sannan kuma aka ikin ruwa da tabo tun daga , mantar dani, kuma hakika na ganni inayin Sujada a cikin tabo da ruwa safiyarta , to ku nemi riskarta a cikin goman karshe na watan.
Ingantacce neBukhari da Muslim suka Rawaito shi - 4540
Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan
Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi - 4545
Ina ganin mafarkenku haƙiƙa sun haɗu a bakwan ƙarshe, duk wanda ya kasance zai yi kardadonsa to ya yi kardadonsa a bakwan ƙarshe
Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi - 4944
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso
Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi