Hadisai

Ina ganin mafarkenku haƙiƙa sun haɗu a bakwan ƙarshe, duk wanda ya kasance zai yi kardadonsa to ya yi kardadonsa a bakwan ƙarshe

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا: أَنَّ رِجَالًا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أُرُوا لَيْلَةَ القَدْرِ فِي المَنَامِ فِي السَّبْعِ الأَوَاخِرِ، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَرَى رُؤْيَاكُمْ قَدْ تَوَاطَأَتْ فِي السَّبْعِ الأَوَاخِرِ، فَمَنْ كَانَ مُتَحَرِّيهَا فَلْيَتَحَرَّهَا فِي السَّبْعِ الأَوَاخِرِ».

Fassara

Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Cewa wasu mazaje daga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an nuna musu daren Lailatul-ƙadr a cikin mafarki a bakwan ƙarshe, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ina ganin mafarkenku haƙiƙa sun haɗu a bakwan ƙarshe, duk wanda ya kasance zai yi kardadonsa to ya yi kardadonsa a bakwan ƙarshe".

Sharhi

Wasu mazaje daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun gani a cikin mafarki cewa daren Lailatul-ƙadr yana kasancewa ne a ƙarshen daren bakwai na Ramadan. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ina ganin mafarke-mafarkenku haƙiƙa sun dace a bakwan ƙarshe na Ramadan, wanda ya kasance yana nufinsa, yana mai kwaɗayi akan nemansa, to sai ya yi ƙoƙari a kardadonsa da nemansa da yawaitawa daga aiki na gari shi ya fi ƙaunar ya zama a bakwan ƙarshe, shi yana farawa ne daga daren ashirin da huɗu idan watan Ramadan ya zama kwana talatin ne, kuma daren ashirin da uku yana farawa ne idan watan ya zama mai kwana ashirin da tara ne.

Fa'idoji

  • Falalar daren Lailatul-ƙadr da kwaɗaitarwa akan kardadonsa.
  • Daga hikimar Allah da rahamarSa cewa Ya ɓoye wannan daren dan mutane su yi ƙoƙari a cikin ibada, dan nemansa, sai ladansu ya yi yawa.
  • Lailatul-ƙadr a cikin goman ƙarshe na Ramadan, kuma ya fi (samun) ƙauna a bakwan ƙarshe daga gare shi.
  • Daren Lailatul-ƙadr ɗaya ne daga dararen goman ƙarshe na Ramadan, shi ne daren da Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da AlKur'ani a cikinsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma Ya sanya wannan daren ya fi wata dubu a albarkarsu, da girman darajarsu, da tasirin aiki na gari cikinsu.
  • An anbace shi (Lailatul-ƙadr) da w (Dal) ɗauri da hakan, kodai daga ɗaukaka ne sai a ce: Wane mai girman daraja ne, sai raɓa daren ya zama daga raɓawar abu ne zuwa siffarsa, wato dare maɗaukaki, yana nufin cewa shi mai girman daraja ne a ɗaukaka da bunƙasa da matsayi har zuwa ƙarshensa, (Lallai ne mu Mun saukar da shi a cikin wani dare mai albarka) [al-Dukhan: 3], ko kuma daga ƙaddarawa ne; Sai raɓawarsa zuwa gareshi ta zama daga raɓawar Zarfi ne zuwa abinda ya tattaroshi, wato wannan daren wanda ƙaddara abinda yake gudana cikin shekara yake kasancewa a cikinsa, (A cikinsa ne ake rarrabe kowane al'amari abin hukuntawa)) [al-Dukhan: 4].
Sharhi: العربية

رَأى رجالٌ من أصحاب النبيِّ صلى الله عليه وسلم في المنام أنّ ليلة القدر تكون في آخر سبع ليال من رمضان. فقال صلى الله عليه وسلم: أرى رؤياكم قد توافقت في السبع الأواخر من رمضان، فمن كان قاصدًا لها، حريصًا على طلبها، فليجتهد في تَحَرِّيها وطلبها بالإكثار من العمل الصالح فهي أرجى أن تكون في السبع الأواخر، وهي تبدأ من ليلة أربع وعشرين إذا كان شهر رمضان ثلاثين يومًا، وتبدأ ليلة ثلاث وعشرين إذا كان الشهر تسعة وعشرين يومًا.

  • فضل ليلة القَدْر والحث على تحريها.
  • من حكمة الله ورحمته أخفى هذه الليلة لِيَجِدَّ الناس في العبادة، طلبًا لها، فيَكثُر ثوابُهم.
  • ليلة القَدْر في العشر الأواخر من رمضان، وفي السبع الأواخر منه أرجى.
  • ليلة القدر هي إحدى ليالي العشر الأواخر من رمضان، وهي الليلة التي أنزل الله عز وجل فيها القرآن على النبي صلى الله عليه وسلم، وجعل هذه الليلة خيرًا من ألف شهر في بركتها، وعظيم قدرها، وأثر العمل الصالح فيها.
  • سميت (ليلة القدْر) بسكون الدال بذلك، إما من الشرف فيُقال: فلان عظيم القدر، فتكون إضافة الليلة من باب إضافة الشيء إلى صفته، أي الليلة الشريفة، يعني أنها عظيمة القدر شرفًا وفخامة ومكانة إلى آخره، ﴿ إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُبَارَكَةٍ ﴾ [الدخان: 3]، وإما من التقدير: فتكون إضافتها إليه من إضافة الظرف إلى ما يحتويه، أي هذه الليلة التي يكون فيها تقدير ما يجري في السنة، ﴿ فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ ﴾ [الدخان: 4].

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari