Hadisai

Wanda ya farar da (wani abu) daga cikin al'amarinmu wannan abinda ba ya ciknsa to an mayar masa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم: «مَنْ أَحْدَثَ فِي أَمْرِنَا هَذَا مَا لَيْسَ فِيهِ فَهُوَ رَدٌّ» متفق عليه. ولمسلم: «مَنْ عَمِلَ عَمَلًا لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ».

Fassara

Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya farar da (wani abu) daga cikin al'amarinmu wannan abinda ba ya ciknsa to an mayar masa". Daga Muslim: "Wanda ya aikata wani aiki wanda ba ya kan al'amarinmu to shi abin an mayar masa".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya yi kirkira a Addini ko ya aikata wani aikin da wani dalili bai yi nuni akansa ba na Alkur’ani ko hadisi, to shi abin juyarwane akan mai shi ba abin karba ba ne a wurin Allah.

Fa'idoji

  • Ibadu an gina su ne akan abinda ya zo ne kawai a cikin Alkur’ani da sunna, ba zamu bautawa Allah - Madaukakin sarki - ba sai da abinda Ya shara'anta ba da bidi'o'i ko kirkirarrun abubuwa ba.
  • Addini ba ra'ayi ba ne, ko ganin kyan abu, kadai da bin Manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Wannan hadisin dalili ne akan cikar Addini.
  • Bidi'a ita ce dukkanin abinda aka farar a Addini wanda babu shi a lokacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, da sahabbansa na akida ne ko magana ko aiki.
  • Wannan Hadisin tushe ne daga tushen Musulunci, shi kamar ma'auni ne ga ayyuka, kamar yadda kowanne aikin da ba'a nufi zatin Allah - madaukakin sarki - da shi ba, to mai aikata shi ba shi da wani lada, hakanan kowanne aikin da bai zama ya dace da abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi ba to shi abin juyarwa ne akan mai aikata shi.
  • Fararrun abubuwan da aka hana su ne abinda suka kasance na al'amuran Addini, ba na duniya ba.
Sharhi: العربية

يُبَيِّنُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن اخترَعَ في الدِّينِ أو عَمِلَ عملًا لم يَدُل عليه دليلٌ من الكتاب والسنة، فهو مَردودٌ على صاحبِه غير مقبول عند الله.

  • العبادات مبناها على ما جاء في الكتاب والسنة، فلا نعبد الله تعالى إلا بما شَرَعَ لا بالبدع والمُحْدَثات.
  • الدين ليس بالرأي والاستحسان، وإنما بالاتباع للرسول صلى الله عليه وسلم.
  • هذا الحديث دليلٌ على كمال الدين.
  • البدعة هي كل ما أُحْدِثَ في الدين ولم يَكنْ على عهدِ النبي صلى الله عليه وسلم وأصحابه من عقيدةٍ أو قولٍ أو عملٍ.
  • هذا الحديث أصلٌ من أصول الإسلام، وهو كالميزان للأعمال، فكما أنَّ كلَّ عَمَلٍ لا يُراد به وجه الله تعالى، فليس لعامله فيه ثواب، فكذلك كلُّ عمل لا يكون وِفْقَ ما جاء به رسول الله صلى الله عليه وسلم فهو مردود على عامله.
  • المُحْدَثات المنهي عنها ما كان من أمور الدين وليس الدنيا.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari