Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عن الْأَغَرِّ رضي الله عنه، وَكَانَ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا أَيُّهَا النَّاسُ تُوبُوا إِلَى اللهِ، فَإِنِّي أَتُوبُ فِي الْيَوْمِ إِلَيْهِ مِائَةَ مَرَّةٍ».
Fassara
Daga Agar - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Manzon Allah - tsiar da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umartar mutane da yawaita tuba da istigfari, kuma yana bada labari game da kansa cewa shi yana tuba zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - kuma yana neman gafararSa a yini sama da sau ɗari, alhali haƙiƙa an gafarta masa abinda ya gabatar na zunubinsa da abinda ya jinkirta, a cikin hakan akwai cikar kankan da kai da bauta ga Allah - Maɗaukaki -.
Fa'idoji
- Kowane mutum duk yadda matsayinsa da darajarsa suka kai a imani, to shi yana buƙatuwa zuwa komawa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -, da cika kansa da tuba, kuma babu wanda ba ya wofinta daga kasawa a tsayuwa da haƙƙin Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -: (Ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya yaku muminai).
- Tuba a game daidai ne daga aikata abubuwan da aka haramta ne da zunubai ko daga kasawa ne a aikata wajibai.
- Ikhlasi a cikin tuba sharaɗi ne akan karbar tuban, wanda ya bar wani zunubi ba dan Allah ba to ba ya kasancewa mai tuba.
- AlNawawi ya ce: A kwai sharuɗɗa uku ga tuba: Ya bar aikata saɓo, kuma ya yi nadama akan aikata shi, kuma ya ƙudirci niyya a yanke cewa ba zai koma ba zuwa tamkarta ba har abada, idan saɓon yana rataye ne da ɗan Adam to yana da sharaɗi na huɗu, shi ne: Maida abinda aka zalinta zuwa ga mai shi, ko tabbatar da kuɓuta daga gare shi.
- Faɗakarwa akan neman gafarar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya lazimtar cewa ya kasance dan wasu zunuban da ya aikata su ne, sai dai hakan dan cikar ubudiyyarsa ne da kuma danfaruwa da ambatanSa - tsarki ya tabbatar maSa - da jinsa girman haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - da kasawar bawa duk aikin da ya aikata a godiyar ni'imominSa, hakan yana daga babin shara'antawa ga al'umma a bayansa ne, zuwa wanin hakan daga hikimomi.
Sharhi: العربية
يَأْمُرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم الناسَ بالإكثار مِن التوبة والاستغفار، ويُخْبِرُ عن نفسه أنه يتوب إلى الله تعالى ويستغفره في اليوم أكثر من مائة مرة، وقد غُفِر له ما تقدم من ذنبه وما تأخر، وفي ذلك كمال الذُّلِّ والتعبد لله جل وعلا.
- كلُّ أحدٍ مهما كانت مرتبته ودرجته في الإيمان، فإنَّه يحتاج إلى الرجوع إلى الله تبارك وتعالى، وتكميل نفسه بالتوبة، وأنَّ كلَّ أحدٍ لا يخلو من تقصيرٍ في القيام بحقِّ الله تبارك وتعالى: (وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ).
- التوبة عامة سواء من فعل المحرّمات والذنوب أو من التقصير في فعل الواجبات.
- الإخلاص في التوبة شرط في قبولها، فمن ترك ذنبًا لغير الله لا يكون تائبًا.
- قال النووي: للتوبة ثلاثة شروط: أن يُقْلِع عن المعصية، وأن يَندم على فعلها، وأن يَعزم عزمًا جازمًا ألَّا يعود إلى مثلها أبدًا، فإن كانت المعصية تتعلق بآدمي فلها شرط رابع، وهو: رَدُّ الظلامة إلى صاحبها، أو تحصيل البراءة منه.
- التنبيه على أن استغفار النبي صلى الله عليه وسلم لا يلزم أن يكون لذنوب ارتكبها، ولكن ذلك لكمال عبوديته وتعلقه بذكره سبحانه، واستشعاره عظم حق الله تعالى وتقصير العبد مهما عمل في شكر نعمه، وهو من باب التشريع للأمة من بعده، إلى غير ذلك من الحكم.