Hadisai

Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنهما أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ أَكَلَ ثُومًا أَوْ بَصَلًا، فَلْيَعْتَزِلْنَا -أَوْ قَالَ: فَلْيَعْتَزِلْ- مَسْجِدَنَا، وَلْيَقْعُدْ فِي بَيْتِهِ»، وَأَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أُتِيَ بِقِدْرٍ فِيهِ خَضِرَاتٌ مِنْ بُقُولٍ، فَوَجَدَ لَهَا رِيحًا، فَسَأَلَ فَأُخْبِرَ بِمَا فِيهَا مِنَ البُقُولِ، فَقَالَ قَرِّبُوهَا إِلَى بَعْضِ أَصْحَابِهِ كَانَ مَعَهُ، فَلَمَّا رَآهُ كَرِهَ أَكْلَهَا، قَالَ: «كُلْ فَإِنِّي أُنَاجِي مَنْ لاَ تُنَاجِي». ولِمُسْلِمٍ عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللهِ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ أَكَلَ مِنْ هَذِهِ الْبَقْلَةِ، الثُّومِ - وقَالَ مَرَّةً: مَنْ أَكَلَ الْبَصَلَ وَالثُّومَ وَالْكُرَّاثَ فَلَا يَقْرَبَنَّ مَسْجِدَنَا، فَإِنَّ الْمَلَائِكَةَ تَتَأَذَّى مِمَّا يَتَأَذَّى مِنْهُ بَنُو آدَمَ».

Fassara

Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa", kuma cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an zo masa da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa daga maɓungura ƙasa, sai ya ji wari daga gareta, sai ya yi tambaya sai aka ba shi labarin abinda ke cikinta na maɓungura ƙasa, sai ya ce ku kusantar da ita ga wani daga sahabbaina wanda ke tare da shi, lokacin da ya ganta sai ya ƙyamaci cinta, ya ce: "Ka ci domin cewa ni ina ganawa da wanda ba ka ganawa (da shi)". A riyawayar Muslim daga Jabir ɗan Abdullahi, daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci daga waɗannan maɓungura ƙasan, tafarnuwa - wani lokacin kuma ya ce: Wanda ya ci albasa da tafarnuwa da algarif to kada ya kusanci masallacinmu, domin mala'iku suna cutuwa da abinda 'ya'yan Adam suke cutuwa da shi".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya ci tafarnuwa ko albasa zuwa masallaci, dan kada ya cutar da 'yan uwansa daga waɗanda suka halarci sallar jam’i da warinsu, shi hanine na tsarkakewa daga zuwa masallaci, ba dan an hana cinsu ba: domin cewa su suna daga abubuwan da aka halatta, haƙiƙa an zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa, lokacin da ya shaƙi wari a cikinta kuma aka ba shi labarin abinda ke cikinta sai ya hanu daga cinta ya kuma kusantar da ita ga wani daga sahabbansa dan ya ci daga gareta, sai ya kyamaci ci dan koyi da shi, lokacin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gan shi ya ce: Ka ci; domin cewa ni ina ganawa da Mala’iku idan sun zo da wahayi. kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mala'iku suna cutuwa daga warin da ake ƙi, kamar yadda mutane suke cutuwa daga gare shi.

Fa'idoji

  • Hanin zuwa masallaci ga wanda ya ci tafarnuwa, ko albasa, ko algarif.
  • Ana riskar da waɗannan abubuwan, dukkan abinda yake da warin da masallata suke cutuwa daga gare shi, kamar warin taba da wiwi da makancin hakan.
  • Illar hanin “wari”, idan ya gushe da yawan dafuwa ko wanin hakan; to karhancin ya gushe.
  • Karhancin cin waɗannan abubuwan ga wanda zuwa sallah a masallaci ya wajaba akansa; dan kada jam'i ya wuce shi a cikin masallaci, muddin dai bai ci ba dan dabara akan kin halarta, to (cin) ya haramta.
  • Hanuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga cin tafarnuwa da makancinsa, badan haramcinsa ba ne, kawai dan ganawarsa ne da (mala'ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -.
  • Kyakkyawan koyarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda yake haɗa hukunci da bayanin sababinsa; dan wanda ake magana ya nutsu da sanin hikimar.
  • Alkali ya ce: Malamai sun ƙiyasta wanin masallaci akan wuraren haɗuwa dan yin sallah, kamar wurin sallar idi da jana'iza da makancinsu daga wuraren taruwa dan yin ibadu, haka nan wuraren taruwa na ilimi da zikiri da walimomi da makancinsu, ba za'a riskar da kasuwanni da wasunsu da su ba.
  • Malamai sun ce: A cikin wannan hadisin akwai dalili akan hana cin tafarnuwa da makamancinta daga shiga masallaci - koda ya kasance ba kowa - domin shi guri ne na mala'iku, kuma saboda gamewar hadisan.
Sharhi: العربية

نَهَى النبيُّ صلى الله عليه وسلم مَن أَكلَ ثومًا أو بَصلًا أن يأتي المسجد، حتى لا يؤذيَ إخوانَه ممن يحضرون صلاة الجماعة بريحهما، وهو نهيُ تنزيهٍ عن إتيان المسجد، لا عن أكلِهما؛ لأنهما من الأطعمة المباحة، وقد أُتيَ صلى الله عليه وسلم بِقِدْرٍ فيه خضروات، فلما شمَّ فيها ريحًا وأُخبِر بما فيها امتنع مِن أكلِها وقَرَّبها إلى بعض أصحابه ليأكل منها، فكره الأكل اقتداء به، فلما رآه صلى الله عليه وسلم قال: كُلْ؛ فإني أناجي الملائكة بالوحي. وأَخبرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أن الملائكة تتأذّى من الروائح الكريهة، كما يتأذى الناس منها.

  • النهي عن إتيان المساجد لمن أكل ثومًا، أو بصلًا، أو كراثًا.
  • يلحق بهذه الأشياء، كلّ ذي رائحة كريهة يتأذى منها المصلون، كرائحة الدُّخان والتَّبْغِ ونحو ذلك.
  • علة المنع الرائحة، فإذا زالت بكثرة الطبخ أو بغير ذلك؛ زالت الكراهة.
  • كراهة أكل هذه الأشياء لمن عليه حضور الصلاة في المسجد؛ لئلا تفوته الجماعة في المسجد، ما لم يأكلها حيلة على إسقاط الحضور، فيحرم.
  • امتناع النبي صلى الله عليه وسلم عن أكل الثوم ونحوه، ليس لتحريمه، وإنما لمناجاته جبريل عليه السلام.
  • حسن تعليم النبي صلى الله عليه وسلم، حيث يَقرُن الحكم ببيان سببه؛ ليطمئن المخاطَب بمعرفة الحكمة.
  • قال القاضي: وقاس العلماء على هذا مجامع الصلاة غير المسجد كمصلّى العيد والجنائز ونحوها من مجامع العبادات، وكذا مجامع العلم والذكر والولائم ونحوها، ولا يلتحق بها الأسواق ونحوها.
  • قال العلماء: وفي هذا الحديث دليل على منع آكل الثوم ونحوه من دخول المسجد -وإن كان خاليًا- لأنه مَحلُّ الملائكة، ولعموم الأحاديث.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari