Hadisai

Mayafin musulmi zuwa rabin ƙwauri ne, kuma babu laifi - ko babu zunubi - a tsakanin sa da idan sawu, kuma abinda ya zama ƙasa da idan sawu to shi yana cikin wuta, wanda ya ja mayafinsa (ƙasa) dan girman kai to Allah ba zai yi duba zuwa gareshi ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad

Rubutun Larabci

عَنْ أبي سَعيدٍ الخُدريَّ رضي الله عنه قال: قال رسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم ِ: «إزْرَةُ المُسْلمِ إلى نصفِ السَّاق، وَلَا حَرَجَ -أو لا جُنَاحَ- فيما بينَهُ وبينَ الكعبينِ، وما كان أسفلَ منَ الكعبين فهو في النار، مَن جرَّ إزارَهُ بطرًا لم يَنْظُرِ اللهُ إليه».

Fassara

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mayafin musulmi zuwa rabin ƙwauri ne, kuma babu laifi - ko babu zunubi - a tsakanin sa da idan sawu, kuma abinda ya zama ƙasa da idan sawu to shi yana cikin wuta, wanda ya ja mayafinsa (ƙasa) dan girman kai to Allah ba zai yi duba zuwa gareshi ba".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mayafin (tufafin) namiji musulmi, shi ne dukkan abinda yake suturta rabin ƙwauri na ƙasa daga maza, halaye uku ne: Na farko: Abinda yake mustahabbi shi ne ya zama zuwa rabin ƙwauri. Na biyu: Wanda ya halatta ba tare da karhanci ba shi ne abinda ke ƙasansa (ƙwauri) zuwa idan sawu; sune ƙasusuwa biyu masu bayyana a mararrabar ƙwauri da diga-digi. Na uku: Wanda aka haramta shi ne ya zama ƙasa da idan sawu, kuma ana jiye masa tsoron kar wuta ta taɓa shi, idan kuma ya zama dan girman kai ne da nishaɗi da shisshigi to Allah ba zai yi duba zuwa gare shi ba.

Fa'idoji

  • Wannan siffar da kuma narkon ya keɓanci maza ne kawai, amma mata to antogance su daga hakan; domin cewa su an umarce su da suturta dukkan jikinsu.
  • Dukkan abinda ke suturta rabin ƙasa daga maza to ana ce masa mayafi; kamar wando, da tufa da waninsu, kuma shi ya shiga cikin hukunce-hukunce na shari'a abin ambata a cikin wannan hadisin.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أن الرجل المسلم لإزاره، وهو كل ما يستر النصف الأسفل من الرجال، ثلاثة أحوال: الأولى: المستحب بأن يكون إلى نصف الساق. الثانية: الجائز بلا كراهة وهو ما تحته إلى الكعبين؛ وهما العظمان البارزان عند مفصل الساق والقدم. الثالثة: المحرَّم بأن يكون أسفل من الكعبين، ويخشى عليه أن تصيبه النار، وإن كان تكبرًا وفرحًا وطغيانًا لم ينظر الله إليه.

  • هذه الصفة والوعيد خاص بالرجال أما النساء فيستثنين من ذلك؛ لأنهن مأمورات بستر جميع جسدهن.
  • كل ما يستر النصف الأسفل من الرجال يسمى إزارًا؛ كالسراويل، والثياب وغيرهما، وهو داخل في الأحكام الشرعية المذكورة في هذا الحديث.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari