Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَثَلُ الْمُؤْمِنِينَ فِي تَوَادِّهِمْ وَتَرَاحُمِهِمْ وَتَعَاطُفِهِمْ مَثَلُ الْجَسَدِ، إِذَا اشْتَكَى مِنْهُ عُضْوٌ تَدَاعَى لَهُ سَائِرُ الْجَسَدِ بِالسَّهَرِ وَالْحُمَّى».
Fassara
Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa yana wajaba halin musulmai sashinsu tare da sashi ya zama da son alheri da tausayi da taimakekeniya da taimako, da jin zafin abinda ya faru gare su na cuta kamar jiki daya ne, idan wata gaba ta yi rashin lafiya daga gare shi , sai jikin ya dauka gaba dayansa da rashin bacci da zazzabi.
Fa'idoji
- Yana kamata girmama hakkokin musulmai da kwadaitarwa akan taimakekeniyarsu da tausayin junansu.
- Yana kamata soyayya da taimako su kasance tsakanin ma'abota imani.
Sharhi: العربية
بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنّه يَجبُ أنْ تكونَ حالُ المسلمين بعضهم مع بعض من محبة الخير والرحمة والمساعدة والنصرة، والتأذِّي بما يحصل لهم من الضرر، كمثل الجسد الواحد، إذا مرض منه عضو، تفاعل معه الجسدُ كلُّه بالسهر والحُمّى.
- ينبغي تعظيمُ حقوق المسلمين والحضُّ على تعاونهم وملاطفة بعضهم بعضًا.
- ينبغي أن يكونَ بين أهلِ الإيمان المحبة والنصرة.