Hadisai

Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi girma a wurin Allah? ya ce: " Ka sanyawa Allah kishiya alhali Shi Ya halicceka

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قال: سَأَلْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ الذَّنْبِ أَعْظَمُ عِنْدَ اللهِ؟ قَالَ: «أَنْ تَجْعَلَ لِلهِ نِدًّا وَهُوَ خَلَقَكَ» قُلْتُ: إِنَّ ذَلِكَ لَعَظِيمٌ، قُلْتُ: ثُمَّ أَيُّ؟ قَالَ: «وَأَنْ تَقْتُلَ وَلَدَكَ؛ تَخَافُ أَنْ يَطْعَمَ مَعَكَ» قُلْتُ: ثُمَّ أَيُّ؟ قَالَ: «أَنْ تُزَانِيَ حَلِيلَةَ جَارِكَ».

Fassara

Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi girma a wurin Allah? ya ce: " Ka sanyawa Allah kishiya alhali Shi Ya halicceka" Na ce: Lallai wannan mai girmane, na ce: Sannan wanne? Ya ce: "Ka kashe danka; dan tsoron ya ci tare da kai". Na ce: Sannan wanne? ya ce: "Ka yi zina da matar makocinka".

Sharhi

Antambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga mafi girman zunubai sai ya ce: Mafi girmansu babbar shirka, ita ce ka sanya tamka ko kini ga Allah a AllantakarSa ko UbangidantakarSa ko sunayenSa da siffofinSa, wannan laifin Allah - Madaukakin sarki - ba ya gafartashi saida tuba, idan mai aikata shi ya mutu akansa to shi madawamine a cikin wuta. Sannan mutum ya kashe dansa dan tsoron ya ci tare da shi, kashe rai kuwa haramun ne, saidai zunubinsa yana girmama idan wanda aka kashe din yana da alaka ta jini da wanda ya yi kisan, kuma zunubinsa yana girmama yayin da manufar wanda ya yi kisan ta zama dan tsoron ya yi tarayya da wanda aka kashe din ne a arzzikin Allah. Sannan mutum ya yi zina da matar makocinsa shi ne ya yi kokarin rudar da matar makocinsa har ya yi zina da ita ta mika wuya gare shi . Zina haramun ce , saidai zunubinta yana girmama idan wacce aka yi zinar da ita matar makoci ce wanda shari'a ta yi wasicci da kyautatawa zuwa gareshi da yi masa kirki da kayauta zama da shi.

Fa'idoji

  • Fifikon zunubai a girma, kamar yadda ayyuka na gari ma suna fifko a falala.
  • Mafi girman zunubai: Yi wa Allah - Madaukakkin sarki - shirka, sannan kashe da don tsoron ya ci tare da kai, sannan ka yi zina da matar makocinka.
  • Arziki yana hannun Allah tsarki ya tabbatar maSa, Ya yi lamuni da azurta ababen halitta.
  • Girman hakkin makwabci, kuma cutar da shi, shi ne mafi girman zunubi daga cutar da waninsa.
  • Mahalicci Shi ne macancanci ga bauta, Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya.
Sharhi: العربية

سُئِلَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن أَعْظَمِ الذنوب فقال: أعظمُها الشركُ الأكبر، وهو أن تجعل لله مَثِيْلًا أو نظيرًا في ألوهيته أو ربوبيته أو أسمائه وصفاته، وهذا الذنب لا يغفره الله تعالى إلا بالتوبة، وإن مات صاحبه عليه فهو مُخَلَّدٌ في النار. ثم قَتْلُ المرءِ ولدَه خشيةَ أن يأكل معه، وقتلُ النفس حرام، لكن يعظم إثمه إذا كان المقتول ذا رَحِمٍ من القاتل، ويعظم إثمه أيضًا حين يكون مقصودُ القاتل الخشيةَ من أنْ يشاركه المقتول في رزق الله. ثم أنْ يُزانيَ الرجل بزوجة جاره بأنْ يُحاول التَّغْرِيرَ بزوجة جاره حتى يَزنيَ بها وتنقاد له، والزنا حرام ولكن يعظم إثمه إذا كانت المزنيُّ بها زوجةَ الجار الذي أوصى الشرع بالإحسان إليه وبره وحسن صحبته.

  • تفاوت الذنوب في العِظَم، كما أن الأعمال الصالحة تَتَفاوت في الفضل.
  • أعظم الذنوب: الشرك بالله تعالى، ثم قتل الولد خشية أن يطعم معك، ثم أن تُزاني زوجة جارك.
  • الرزق بيد الله وقد تَكَفَّلَ سبحانه بأرزاق المخلوقين.
  • عِظَم حق الجار، وأنَّ أذيتَه أَعظم إثمًا من أذية غيرِه.
  • الخالق هو المستحق للعبادة وحده لا شريك له.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari