Hadisai

Allah ba Ya duba zuwa wanda ya ja tufansa (ƙasa) dan girman kai

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «لاَ يَنْظُرُ اللَّهُ إِلَى مَنْ جَرَّ ثَوْبَهُ خُيَلاَءَ».

Fassara

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa wanda ya ja tufansa (ƙasa) dan girman kai".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga sakin tufafi ko gwabso ƙasan idan sawu dan jiji da kai da kuma girman kai, kuma cewa wanda ya aikata hakan ya kasance ya cancanci narko mai tsanani cewa Allah ba Zai yi duba zuwa gareshi ba duba na rahama a ranar alƙiyama.

Fa'idoji

  • Tufafi ya ƙunshi dukkan abinda yake suturta jiki daga wando da tufa da mayafi da wasunsu.
  • Hani daga sakin tufa ya ja ƙasa ya keɓanci namiji ne kawai, Nawawi ya ce: Malamai sun yi ijma'i akan halaccin sakin tufafi ya ja ƙasa ga mata, haƙiƙa izini garesu (mata) a sakin bezar kayansu zuwa zira'i ya inganta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Ibnu Baaz ya ce: Sakin tufafi ya ja ƙasa abin hanawa ne kuma haramun ne dan gamewar hadisan, amma uƙuba to ita daban daban ce ba ya lazimta ta zama madaidaiciya, domin wanda ya yi nufin girman kai bai zama kamar wanda bai yi nufin girman kai ba.
  • Ibnu Baaz ya ce: Mace al'aura ce babu mai hanata sakin tufafinta taku ɗaya, idan bai isheta ba to ta sake shi zira'i tun farko daga idan sawu.
  • AlKali ya ce: Malamai sun ce: A dunƙule an ƙi dukkan abinda ya ƙaru akan buƙata da al'ada a cikin tufafi na tsawaitawa da yalwatawa, Allah ne Mafi sani.
  • AlNawawi ya ce: Gwargwado abin so a abinda gefen riga da mayafi zai sauka gare shi to rabin ƙwauri ne, babu laifi a kansa a abinda ke tsakaninsa da tsakanin idan sawu, abinda ya yi ƙasa da hakan to shi yana cikin wuta, abinda ake so shi ne rabin ƙwauri, abinda ya halatta babu karhanci shi ne abinda ke ƙasansa zuwa idan sawu, abinda ya sauka daga idan sawu to abin hanawa.
  • Ibnu Usaimin ya faɗa akan faɗinsa: (Allah ba Ya duba zuwa gare shi) wato duba na rahama da tausayi, ba ana nufi da shi: Gamammen duba ba; domin cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - wani abu ba ya ɓuya gareShi kuma wani abu ba ya fakuwa daga ganinSa, sai dai abin nufi duba na rahama da tausayi.
Sharhi: العربية

حَذَّرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم مِن إِرْخَاءِ الثوب أو الإزَارِ أَسفل الكعبين عُجبًا وكبرًا، وأنّ مَن فعل ذلك كان مُستحِقًّا للوعيد الشديد بأن لا ينظر الله إليه يوم القيامة نَظَرَ رَحمة.

  • الثوب يَشمل كلَّ ما يَستُر أسفل البدن من سروال وثوب وإزار وغيرها.
  • النهي عن الإسبال خاصٌّ بالرجال، قال النووي: وأجمع العلماء على جواز الإسبال للنساء، وقد صح عن النبي صلى الله عليه وسلم الإذنُ لهنَّ في إرخاء ذُيُولِهنّ ذراعًا.
  • قال ابن باز: الإسبال ممنوع ومحرم لعموم الأحاديث، وأما العقوبة فهي متفاوتة ولا يلزم أن تكون مُتساوية، فإنه ليس مَن قَصَدَ الخيلاء كمن لم يَقصد.
  • قال ابن باز: المرأة عورة فلا مانع من إرخائها شِبْرًا، فإن لم يَكفِها أَرْخَتْ ذِراعًا ابتداءً من الكَعْب.
  • قال القاضي: قال العلماء: وبالجملة يكره كل ما زاد على الحاجة والمعتاد في اللباس من الطول والسعة، والله أعلم.
  • قال النووي: القَدْر المستحب فيما يَنزل إليه طرف القميص والإزار فنصف الساقين، ولا جناح عليه فيما بينه وبين الكعبين، وما أسفل من ذلك فهو في النار، فالمستحب نصف الساقين، والجائز بلا كراهة ما تحته إلى الكعبين، فما نزل عن الكعبين فهو ممنوع.
  • قال ابن عثيمين على قوله: (لا ينظر الله إليه) أي نَظَرَ رَحمةٍ ورَأْفَة، وليس المراد به: النظر العام؛ لأن الله سبحانه وتعالى لا يخفى عليه شيء ولا يغيب عن بصره شيء، لكن المراد نظر الرحمة والرأفة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari