Hadisai

An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Hasan ne kuma IngantacceTirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سُئِلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنْ أَكْثَرِ مَا يُدْخِلُ النَّاسَ الْجَنَّةَ، فَقَالَ: «تَقْوَى اللهِ وَحُسْنُ الْخُلُقِ»، وَسُئِلَ عَنْ أَكْثَرِ مَا يُدْخِلُ النَّاسَ النَّارَ فَقَالَ: «الْفَمُ وَالْفَرْجُ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u", kuma an tambayeshi game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane wuta sai ya ce: "Baki da farji".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - yana bayyana cewa mafi giman sabubban da suke shigar da mutane aljanna sabubba biyu ne, sune: Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u. Tsoron Allah: Shi ne ka sanya kariya tsakaninka da tsakanin azabar Allah, ta hanyar aikata umarninsa da nisantar hane-hanensa. Kyakkyawar ɗabi'a: Tana kasancewa ne da shinfiɗar fuska, da yin aikin kirki, da kamewa daga cuta. Kuma mafi girman sabubban da suke shigarwa wuta sabubba biyu ne, su ne: Harshe da farji. yana daga saɓon harshe: Ƙarya, da raɗa, da annamimanci da wasunsu. Yana daga saɓon farji: Zina da luwaɗi da wasunsu.

Fa'idoji

  • Shiga aljanna yana da sabubban da suka rataya da Allah - Maɗaukakin sarki, daga cikinsu akwai: Tsoronsa, da kuma sabubban da suke rataya da mutane, daga cikinsu akwai: Kyawawan ɗabi'u.
  • Hatsarin harshe ga mai shi, kuma yana daga sabubban shiga wuta.
  • Hatsarin sha'awe-sha'awe da ayyukan alfasha ga mutum, kuma suna daga mafi yawan sabubban shiga wuta.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ أعظم الأسباب التي تُدخل الجنة سببان، هما: تقوى الله وحسن الخلق. فتقوى الله: هي أن تجعل بينك وبين عذاب الله وقاية، وذلك بفعل أوامره واجتناب نواهيه. وحسن الخلق: يكون ببسط الوجه وبذل المعروف وكف الأذى. وأن أعظم الأسباب التي تدخل النار سببان، هما: اللسان والفرج. فاللسان من معاصيه: الكذب والغيبة والنميمة وغيرها. والفَرْج من معاصيه: الزنى واللواط وغيرها.

  • دخول الجنة له أسباب متعلقة بالله تعالى، ومنها: تقواه، وأسباب متعلقة بالناس، ومنها: حسن الخُلق.
  • خطر اللسان على صاحبه، وأنه من أسباب دخول النار.
  • خطر الشهوات والفواحش على الإنسان، وأنها من أكثر أسباب دخول النار.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari