Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رضي الله عنها أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَّمَهَا هَذَا الدُّعَاءَ: «اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ الْخَيْرِ كُلِّهِ، عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ، مَا عَلِمْتُ مِنْهُ وَمَا لَمْ أَعْلَمْ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ الشَّرِّ كُلِّهِ، عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ، مَا عَلِمْتُ مِنْهُ وَمَا لَمْ أَعْلَمْ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِ مَا سَأَلَكَ عَبْدُكَ وَنَبِيُّكَ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا عَاذَ بِهِ عَبْدُكَ وَنَبِيُّكَ، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْجَنَّةَ، وَمَا قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ النَّارِ، وَمَا قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ، وَأَسْأَلُكَ أَنْ تَجْعَلَ كُلَّ قَضَاءٍ قَضَيْتَهُ لِي خَيْرًا».
Fassara
Daga (Nana) A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koya mata wannan addu'ar: "Ya Allah ina roƙon Ka dukkan alheri, magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba, kuma ina neman tsarinKa daga dukkan sharri magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba. Ya Allah ina roƙonKa mafi alherin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya roƙeKa, kuma ina neman tsarinKa daga sharrin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya nemi tsarin Ka da shi, ya Allah ina roƙonKa aljanna da abin da yake kusantota na magana ko aiki, kuma ina neman tsarinKa daga wuta, da abin da yake kusantota na magana ko aiki, ina rokonKa Ka sanya dukkan hukuncin da Ka hukunta gare ni ya zama alheri".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koyawa Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - dunkulallun addu'o'i su ne addu'o'i huɗu: Na farko: Addu'a mai game kowane alheri: (Ya Allah ina roƙonKa dukkan alheri) dukkansa, (magaggaucinsa) makusanci a lokacinsa, (da majinkircinsa) na nesa, (abinda na sani daga gare shi) daga abinda Ka sanar da ni, (da abinda ban sani ba), daga abinda yake kasancewa a cikin saninKa - tsarki ya tabbatar maKa -. A cikinsa akwai fawwala al'amari zuwa ga Allah Masani Mai bada labari Mai sawwaƙawa; sai tsarki ya tabbatar maSa Ya zaɓawa musulmi maffificinsa kuma mafi kyansa, (Ina neman tsarinKa) ina neman tsarinKa ina kiyayewa (da Kai daga sharri dukkansa magaggaucinsa da majinkircinsa, abinda na sani da abinda ban sani ba). Addu'a ta biyu: Ita ce kiyayewar musulmi daga ya yi shisshigi a cikin addu'a (Ya Allah lallai ni ina roƙonKa) ina nemanKa (daga mafificin abinda bawanKa kuma AnnabinKa ya roƙeKa) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, (ina neman tsarin Ka) ina fakewa ina nenam tsari (da Kai daga sharrin abinda bawanKa kuma AnnabinKa ya nemi tsarin Ka) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi , wannan addu'a ce da nema daga Allah Ya bawa mai addu'ar daga abinda Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya roƙe shi kuma ya neme shi ga kansa, ba tare da ƙididdiga nau'ikan abinda tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi ya roka ba. Addu'a ta uku: Neman shiga aljanna da nisantar wuta, shi abin neman kowane musulmi ne kuma matuƙar aikinsa: (Ya Allah ina roƙon Ka aljanna) da rabauta da ita (da abinda ya kusantota na magana ko aiki) na gari wanda zai yardar da kai, (ina neman tsarinKa daga wuta) inda babu tsari daga munanan ayyuka sai da luɗufinKa, (da abinda ya kusanto zuwa gareta na magana ko aiki) daga saɓon da zai sa fushinKa. Addu'a ta huɗu: Addu'a da yarda da hukuncin Allah (ina roƙonKa Ka sanya kowane hukuncin da Ka hukunta mini ya zama alheri) dukkan al'amarin da Allah Ya hukunta shi gareni Ya sanya shi mafi alheri gare ni, wannan yana daga addu'a da yarda da hukuncin Allah.
Fa'idoji
- Koyarwar mutum ga iyalansa abinda zai anfanar da su daga al'amuran Addini da duniya, kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga (Nana) A'isha.
- Abinda ya fi ga musulmi ya haddace addu'o'in da suka zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa su suna daga addu'o'i dunkulallu.
- Malamai sun faɗa game da wannan hadisin: Shi ne mafi tattarowar hadisai a roƙon alheri da neman tsari daga sharri, shi yana daga kalmomi masu tattarowa (kalmomi kaɗan masu ɗaukar ma'anoni masu yawa) waɗanda aka bawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - su.
- Daga sabubban shiga aljanna bayan rahamar Allah: Ayyuka da kalamai na gari.
Sharhi: العربية
علَّم النبيُّ صلى الله عليه وسلم عائشةَ رضي الله عنها جوامِعَ الدعاء وهو أربع دعوات: الأول: دعاء عام لكل خير: (اللهم إني أسألك من الخير كله) وجميعه، (عاجله) القريب في وقته، (وآجله) البعيد، (ما عَلِمتُ منه) مما علّمتني، (وما لم أعلم)، مما يكون في علمك سبحانك، وفيه تفويض الأمر إلى الله العليم الخبير اللطيف؛ فيختار سبحانه للمسلم أفضله وأحسنه، (وأعوذ) وأعتصم وأَحْتَمي (بك من الشر كله عاجله وآجله، ما علمت منه وما لم أعلم). الدعاء الثاني: وهو حِفْظٌ للمسلم مِن أنْ يَعْتَدي في الدعاء (اللهم إني أسألك) وأطلبك (من خير ما سألك عبدك ونبيك) صلى الله عليه وسلم، (وأعوذ) وألتجئ وأعتصم (بك من شر ما عاذ به عبدك ونبيك) صلى الله عليه وسلم، وهذا دعاء وطَلَبٌ من الله أنْ يُعطيَ الداعي مما سأله وطلبه النبيُّ محمد صلى الله عليه وسلم لنفسه، دون تعديد لأنواع ما دعا به صلى الله عليه وسلم. الدعاء الثالث: طلب دخول الجنة والابتعاد عن النار، وهو مَطْلبُ كلِّ مسلم وغايةُ عَمَلِه: (اللهم إني أسألك الجنة) والفوز بها (وما قرّب إليها من قول أو عمل) صالح يرضيك، (وأعوذ بك من النار) حيث لا عصمة من قبائح الأعمال إلا بلطفك، (وما قرّب إليها من قول أو عمل) من المعاصي التي تغضبك. الدعاء الرابع: الدعاء بالرضا بقضاء الله (وأسألك أن تجعل كل قضاء قضيتَه لي خيرًا) وكلّ أمر قضاه الله لي أن يجعله خيرًا لي، وهذا من الدعاء بالرضا بقضاء الله.
- تعليم الرجل أهلَه ما ينفعهم من أمور الدين والدنيا، كما علم النبي صلى الله عليه وسلم عائشة.
- الأفضل للمسلم أن يحفظ الأدعية الواردة عن النبي صلى الله عليه وسلم؛ لأنها من جوامع الدعاء.
- قال العلماء عن هذا الحديث: هو أجمع حديث في سؤال الخير والاستعاذة من الشر، فهو من جوامع الكَلِمِ التي أوتيها النبي صلى الله عليه وسلم.
- من أسباب دخول الجنة بعد رحمه الله: الأعمال والأقوال الصالحة.