Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما قَالَ: كَانَ مِنْ دُعَاءِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ زَوَالِ نِعْمَتِكَ، وَتَحَوُّلِ عَافِيَتِكَ، وَفُجَاءَةِ نِقْمَتِكَ، وَجَمِيعِ سَخَطِكَ».
Fassara
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ya kasance daga addu'ar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -: "Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga abubuwa huɗu: Na farko: (Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa) ta Addini da duniya kuma in tabbata akan Musulunci, in nisanci faɗawa cikin saɓon da yake gusar da ni'imomi. Na biyu: (Da juyawar lafiyarKa) da canjata zuwa bala'i; to ina roƙonKa dawwamar lafiya, da kuɓuta daga radaɗi da cututtuka. Na uku: (Da shammatar azabarKa) daga bala'i ko saɓo, azaba da uƙuba idan suka zo fuj'a bagtatan, to babu wani lokaci a wannan dan tuba da riska, wanda aka shafa da su zai zama mafi girma kuma mafi tsanani. Na huɗu: (Da dukkan fushinKa) da sabubban da suke wajabta fushinKa; domin wanda Ka yi fushi da shi to haƙiƙa ya taɓe kuma ya yi asara. Haƙiƙa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zo da lafazin jam'i; dan ya ƙunshi sabubban fushinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - daga maganganu da ayyuka da ƙudirce-ƙudierce.
Fa'idoji
- Buƙatuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Waɗannan neman tsarin masu albarka sun ƙunshi: Dacewa ga godewar ni'imomi, da kiyayewa daga afkawa cikin saɓo; domin cewa su suna gusar da ni'imomi.
- Kwaɗayi daga barin nisanta daga guraren fushin Allah - Maɗaukakin sarki -.
- (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nemi tsari daga shammatar azabar Allah - Maɗaukakin sarki -; domin cewa Shi idan Ya yi wa bawa azaba to haƙiƙa Ya saukar masa da bala'in da ba zai iya tunkuɗeshi ba, kuma ba zai nemi kariyar ragowar halittu ba, koda sun taru gaba ɗaya.
- (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nemi tsari daga juyawar lafiyarSa - tsarki ya tabbatar maSa -; domin cewa shi idan Allah ya kasance ya keɓance shi da lafiyarSa to haƙiƙa ya rabauta da alherin duniya da lahira, idan ta juya daga gare shi to haƙiƙa an taɓa shi da sharrin duniya da lahira, domin cewa lafiya da ita ce gyaruwar Addini da duniya (suke).
Sharhi: العربية
اسْتَعاذَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم مِن أربعةِ أمور: الأول: (اللهم إني أعوذ بك من زوال نعمتك) الدينيّة والدنيويّة وأنْ أَثْبُتَ على الإسلام، وأبْتَعِدَ عن الوقوع في المعاصي التي تُزيل النِّعَم. الثاني: (وتَحَوُّل عافيتك) بتبديلِها إلى البلاء؛ فأسألك دوام العافية، والسلامة من الآلام والأسقام. الثالث: (وفجأة نقمتك) من بلاء أو مصيبة، فالنقمة والعقوبة إذا جاءت فجأة وبَغْتَة، لم يكن هناك زمانٌ للتوبة والاستدراك، وكان المُصاب بها أعظمَ وأشدَّ. الرابع: (وجميع سخطك) والأسباب المُوجِبَة لغضبك؛ فإنَّ مَن سَخِطْتَ عليه فَقَد خاب وخَسِر. وقد أتى صلى الله عليه وسلم بلفظ الجَمْع؛ لِتشمَلَ جميعَ أسبابِ سَخَطِهِ سبحانه وتعالى من الأقوال والأعمال والاعتقادات.
- افتقار النبيِّ صلى الله عليه وسلم إلى الله تعالى.
- تضمّنت هذه الاستعاذة المباركة: التوفيق لشكر النِّعم، والحفظ من الوقوع في المعاصي؛ لأنها تزيل النعم.
- الحرص عن الابتعاد عن مواضع سَخَطِ الله تعالى.
- استعاذ صلى الله عليه وسلم من فجأة نقمة الله تعالى؛ لأنه إذا انتقم من العبد فقد أَحَلَّ به من البلاء ما لا يَقدِر على دفعه، ولا يُستدفع بسائر المخلوقين، وإن اجتمعوا جميعًا.
- استعاذ صلى الله عليه وسلم من تحول عافيته سبحانه؛ لأنه إذا كان قد اختصَّه الله بعافيته، فقد ظفر بخير الدارين، فإن تحولت عنه فقد أصيب بشر الدارين، فإن العافية بها صلاح الدِّين والدنيا.