Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِلْأَشَجِّ أَشَجِّ عَبْدِ الْقَيْسِ: «إِنَّ فِيكَ خَصْلَتَيْنِ يُحِبُّهُمَا اللهُ: الْحِلْمُ، وَالْأَنَاةُ».
Fassara
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ga mai tabo mai tabon Abdulƙais: «Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Munzir ibnu A'iz ga mai tabo a fuskar nan na ƙabilar Abdulƙais kuma shugabanta - Allah Ya yarda da shi - Lallai kai kana da siffofi biyu Allah Yana sonsu, sune: Hankali, da kuma tabbata da nutsuwa da kuma rashin gaggawa.
Fa'idoji
- Kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da haƙuri da kuma dangana.
- Kwaɗaitarwa akan tabbata a cikin al'amura da kuma duba ƙarshensu.
- Haƙuri da dangana suna daga cikin siffofi ababen yabo.
- Mutum ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - akan abinda Ya halicce shi akansa na ɗabi'u ababen yabo.
- Kalmar al-Ashaj ita ce wanda aka jiwa rauni a fuska, ko a kai, ko goshi.
Sharhi: العربية
قال النبي صلى الله عليه وسلم للمنذر بن عائذ أشج قبيلة عبد القيس ورئيسها رضي الله عنه: إن فيك صفتين يحبهما الله، وهما: العقل، والتثبت والوقار وعدم العجلة.
- الحث على التخلق بالحلم والأناة.
- الحض على التثبت في الأمور والنظر في العواقب.
- الحلم والأناة من الصفات الحميدة.
- حمد الإنسان لله تعالى على ما جبله عليه من الأخلاق الحميدة.
- الأشج من أصيب بجُرح في الوجه، أو الرَّأس، أو الجبين.