Hadisai

Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ciyar zan ciyar da kai

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «قَالَ اللهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ أُنْفِقْ عَلَيْكَ».

Fassara

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ciyar zan ciyar da kai.

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin Allah maɗaukakin sarki Ya ce: Ya kai Ɗan Adam ka ciyar cikin ciyarwar wajibi da ta Mustahabbi zan yalwata maka, zan kuma ba ka makwafin abin da ka bayar, kuma in sanya maka albarka.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa a kan sadaka da kuma ciyarwa Fi-sabilillahi.
  • Ciyarwa ta ɓangarorin alheri yana daga cikin manyan dalilan samun albarka a arziki da kuma ninka shi, da kuma yadda Allah zai mayarwa bawa abin da ya ciyar.
  • Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaitoshi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu keɓance-keɓancen Alkur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karantashi, da yin tsarki sabo da shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.
Sharhi: العربية

يَخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ الله تبارك وتعالى قال: أنفق يا ابن آدم -من النفقات الواجبة والمستحبة- أُوَسِّعْ عليك وآتِك عِوَضًا عن ذلك وأباركْ لك فيه.

  • الحث على الصدقة والإنفاق في سبيل الله.
  • الإنفاق في وجوه الخير من أعظم أسباب البركة في الرزق ومضاعفته، وإخلاف الله على العبد ما أنفقه.
  • هذا الحديث مما يرويه النبي صلى الله عليه وسلم عن ربه، ويسمى بالحديث القدسي أو الإلهي، وهو الذي لفظه ومعناه من الله، غير أنه ليست فيه خصائص القرآن التي امتاز بها عما سواه، من التعبد بتلاوته والطهارة له والتحدي والإعجاز وغير ذلك.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari