Hadisai

Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا: أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ الإِسْلاَمِ خَيْرٌ؟ قَالَ: «تُطْعِمُ الطَّعَامَ، وَتَقْرَأُ السَّلاَمَ عَلَى مَنْ عَرَفْتَ وَمَنْ لَمْ تَعْرِفْ».

Fassara

Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su -: Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba".

Sharhi

An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wadanne dabi'u ne na Musulunci suka fi? sai ya ambaci dabi'u biyu: Na farko: Yawaita ciyar da abin ci ga talakawa, sadaka da kyauta da saukar bako da walima za su shiga ciki, falalar ciyarwa tana karfafa alokutan yunwa da tsadar farashi. na biyu: Yin sallama ga kowanne musulmi, ka san shi ko ba ka san shi ba.

Fa'idoji

  • Kwadayin sahabbai akan sanin dabi'un da zasu anfanar a duniya da lahira.
  • Sallama da ciyar da abinci suna daga mafifitan ayyuka; Dan falalarsu da bukatuwar mutane garesu a kowanne lokaci.
  • Da wadannan dabi'un ne kyautatawa take taruwa da fada da aikatawa, kuma ita ce mafi cikar kyautatawa.
  • Wadannan dabi'un a cikin abinda yake rataya ne na mu'amalantar musulmai a tsakaninsu, akwai wasu dabi'un na mu'amalantar bawa ga Ubangijinsa.
  • Farawa da sallama abin kebancewa ne tsakanin musulmai, ba'a Farawa kafirai da sallama.
Sharhi: العربية

سُئِلَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم: أيُّ خِصَالِ الإسلامِ أفضلُ؟ فَذَكَرَ خَصْلتين: الأولى: الإكثار من إطعام الفقراء، ويدخل فيه الصدقة والهدية والضيافة والوليمة، وتتأكد فضيلة الإطعام في أوقات المجاعة وغلاء الأسعار. والثانية: إلقاء السلام على كلِّ مسلم، عَرَفْتَه أوْ لم تَعْرِفْه.

  • حرص الصحابة على معرفة الخِصال التي تنفع في الدنيا والآخرة.
  • السلام وإطعام الطعام من أفضل الأعمال في الإسلام؛ لفضلها وحاجة الناس إليها في كل وقت.
  • بهاتين الخصلتين يجتمع الإحسان بالقول والفعل، وهو أكمل الإحسان.
  • هذه الخصال فيما يتعلَّق بتعامل المسلمين فيما بينهم، وهناك خِصالٌ في تعامُلِ العبد مع ربِّه.
  • البدء بالسلام مخصوص بين المسلمين، فلا يُسلَّم ابتداءً على كافر.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari