Hadisai

Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي موسى رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إِنَّ اللهَ لَيُمْلِي لِلظَّالِمِ، حَتَّى إِذَا أَخَذَهُ لَمْ يُفْلِتْهُ» قَالَ: ثُمَّ قَرَأَ: «{وَكَذَلِكَ أَخْذُ رَبِّكَ إِذَا أَخَذَ الْقُرَى وَهِيَ ظَالِمَةٌ إِنَّ أَخْذَهُ أَلِيمٌ شَدِيدٌ}[هود: 102]»

Fassara

Daga Abu Musa Allah Ya yarda da shi ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan cewa ci gaba da zalunci da laifuka da shirka da zaluntar mutane a haƙƙoƙinsu, to, lalle Allah maɗaukaki Yana saurarawa azzalumi ya jinkirta masa, ya tsawaita masa a rayuwarsa da dukiyarsa ba zai gaggauta masa uƙuba ba, to, idan bai tuba ba sai ya damƙe shi, kuma ba zai sake shi ba, ba kuma zai ƙyale shi ba sabo da yawan zaluncinsa. Sannan sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya karanta: Kuma haka damƙar Ubangijinka take idan ya damƙi alƙaryu suna azzalumai, lalle damƙarsa mai raɗaɗi ce kuma mai tsanani ce.

Fa'idoji

  • Ya wajaba ga mai hankali ya yi gaggawar tuba, kuma kada ya lamuncewa kamun Allah, idan ya kasance wanda yake kan aikata zalunci.
  • Jinkirtawar da Allah Yake yi wa azzalumai da kuma rashin gaggauta yi musu uƙuba ɗaurin talala ne garesu, da kuma ninka musu azaba idan ba su tuba ba.
  • Zalunci yana cikin sabubban uƙubar Allah ga al’umma.
  • Idan Allah Ya halakar da gari, to, zai iya yiwuwa akwai mutanen ƙwarai a ciki, to, su waɗannan za’a tashe su a ranar Alkiyama a kan abin da suka mutu akan shi na kyakkyawan aiki, ba zai cutar da su ba dan wannan ukubar ta hada da su.
Sharhi: العربية

يُحَذِّرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم من التَّمادِي في الظلم بالمعاصي والشرك وظلم الناس في حقوقهم، فإن الله تعالى يُمْهِلُ الظالمَ ويؤخِّرُه ويُطيل له في عُمُرِه ومالِه فلا يُعاجِلُه العقوبةَ؛ فإنْ لم يتب أَخَذَه ولم يُطْلِقْه ولم يَتْرُكْه لكثرة ظلمه. ثم قرأ صلى الله عليه وسلم: {وكذلك أخذ ربك إذا أخذ القرى وهي ظالمة إن أخذه أليم شديد} [هود: 102].

  • على العاقل المبادرة إلى التوبة، وأن لا يَأمَنْ من مَكْرِ الله إذا كان مُقيمًا على الظلم.
  • إمهال الله عز وجل للظالمين وعدم مُعاجَلتِهم بالعقوبة استدراجًا لهم ومضاعفة للعذاب إن لم يتوبوا.
  • الظلم من أسباب عقوبة الله للأمم.
  • إذا أهلك الله قرية فقد يكون فيها صالحون، فهؤلاء يُبعثون يوم القيامة على ما ماتوا عليه من الصلاح، ولا يضرهم أنْ شَمِلَتْهم العقوبةُ.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari