Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم قَامَ بَعْدَ أَنْ رَجَمَ الْأَسْلَمِيَّ فَقَالَ: «اجْتَنِبُوا هَذِهِ الْقَاذُورَةَ الَّتِي نَهَى اللَّهُ عَنْهَا فَمَنْ أَلَمَّ فَلْيَسْتَتِرْ بِسِتْرِ اللَّهِ وَلْيُتُبْ إِلَى اللَّهِ، فَإِنَّهُ مَنْ يُبْدِ لْنَا صَفْحَتَهُ نُقِمْ عَلَيْهِ كِتَابَ اللَّهِ عز وجل».
Fassara
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah ya yarda da su - cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bayan ya jefe al-Aslami sai ya ce: "Ku nisanci wannan ƙazantaccan da Allah Ya yi hani gare su, duk wanda ya zakke musu to ya suturta da suturar Allah kuma ya tuba zuwa ga Allah, domin cewa duk wanda ya bayyanar mana da aikinsa zamu tsayar da Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka a kansa".
Sharhi
Ibnu Umar - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe bayan ya jefe Ma'izu ɗan Malik al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - haddin zina, sai ya yi wa mutane huɗuba kuma ya ce: Ku nisanci waɗannan ƙazantar da abinda yake muni saboda saɓon da Allah ya hana aikatasu, wanda ya faɗa kuma ya aikata wani abu daga cikinsu to abubuwa biyu sun wajaba a kansa: Na farko: Ya suturta inda Allah Ya suturta shi kada ya bayar da labarin saɓonsa. Na biyu: Ya yi gaggawar tuba zuwa ga Allah kuma kada ya nace a kansu, wanda saɓonsa ya bayyana garemu zamu tsayar masa da haddin da aka ambata a cikin Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga wannan saɓon.
Fa'idoji
- Kwaɗaitarwa a kan cewa bawa mai zunubi ya suturta kansa, kuma ya tuba daga zunubi a abinda ke tsakaninsa da UbangijinSa.
- Haddi idan ya kai ga shugaba to babu makawa daga tsaida haddin.
- Wajabcin nisantar saɓo, da kuma tuba daga garesu.
Sharhi: العربية
أخبر ابن عمر رضي الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم قام بعد أن رجم ماعز بن مالك الأسلمي رضي الله عنه حدَّ الزنا، فخطب بالناس وقال: اجتنبوا هذه القاذورة وما يُستقذر ويُستقبح من المعاصي التي نهى الله عنها، ومن وقع وأصاب منها شيئًا وجب عليه شيئان: الأول: أن يستتر حيث ستره الله ولا يُخبِر بمعصيته. الثاني: أن يبادر بالتوبة إلى الله ولا يصرّ عليها، ومن ظهرت لنا معصيته أقمنا عليه الحدَّ المذكور في كتاب الله عز وجل لتلك المعصية.
- الترغيب في ستر العبد المذنب نفسه، ويتوب عن الذنب فيما بينه وبين ربه.
- الحدود إذا بلغت ولي الأمر فلا بد من إقامة الحد.
- وجوب اجتناب المعاصي، والتوبة منها.