Hadisai

Ba ya kamata ga wani mutum musulmi da yake da wani abinda zai yi wasiyya da shi, ya kwana darare uku sai wasiyyarsa tana rubuce a wurinsa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهُما أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَا حَقُّ امْرِئٍ مُسْلِمٍ لَهُ شَيْءٌ يُوصِي فِيهِ، يَبِيتُ ثَلَاثَ لَيَالٍ، إِلَّا وَوَصِيَّتُهُ عِنْدَهُ مَكْتُوبَةٌ»، قَالَ عَبْدُ اللهِ بْنُ عُمَرَ رضي الله عنهما: «مَا مَرَّتْ عَلَيَّ لَيْلَةٌ مُنْذُ سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ ذَلِكَ إِلَّا وَعِنْدِي وَصِيَّتِي».

Fassara

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ba ya kamata ga wani mutum musulmi da yake da wani abinda zai yi wasiyya da shi, ya kwana darare uku sai wasiyyarsa tana rubuce a wurinsa", Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: "Wani dare bai taɓa wucewa gareni ba tunda na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya faɗi haka ba sai wasiyyata tana tare da ni".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ba ya kamata ga wani musulmi da yake da wani abinda zai yi wasicci da shi na haƙƙoƙi ko dukiyoyi koda kaɗan ne, ya kwana darere uku, sai wasiyyarsa tana rubuce a wurinsa. Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - Ya ce: Ban taɓa kwana a wani dare ba tunda na ji shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi haka sai wasiyyata tana tare da ni.

Fa'idoji

  • Halaccin wasiyya da gaggawar yinta, dan yin bayani gareta, da kuma ruko da umarnin mai shara'antawa a cikinta, da yi wa mutuwa tanadi, da lura da ita da gurin bada ita, tun kafin wani abu mai shagaltarwa ya shagaltar da shi.
  • Wasiyya: Ma'anarta, ita ce mutum ya alƙwarantawa wani mutum yin tasarrufin wani abu daga dukiyarsa bayan mutuwarsa, ko ya alƙawarantawa wani mutum kan ya kula da 'ya'yansa ƙanana, ko ya alƙawarantawa wani mutum a wani abu daga ayyukan da zai mallakesu bayan mutuwarsa.
  • Wasiyya ta rabu gida uku: 1- Mustabbi, ita ce wasicci da wani abu daga dukiyarsa da za'a bada ita a tafarkin alheri, da kyautatawa; dan ladansa ya sadu da shi bayan mutuwarsa. 2- Ta wajibi, ita ce wasicci da abinda ke kansa na haƙƙoƙi, daidai ne sun kasance haƙƙoƙin Allah ne - Maɗaukaki sarki -, kamar zakkar da ba'a fitar da ita ba, ko kaffara, da makamancinsu daga abinda yake wajaba a asalin shari'a, ko waɗannan haƙƙoƙin sun kasance na 'yan Adam ne; kamar bashi, da maida amanoni. 3- wasiyyar da aka haramta, idan ta ƙaru akan sulusi (ɗaya bisa uku) daga dukiyarsa, ko idan ya yi wasicci ga wani mai gado.
  • Falalar Ɗan Umar - Allah ya yarada da su -, da gaggawarsa zuwa aikata alheri, da bin Mai shara'antawa Mai hikima.
  • Ibnu Daƙiƙul Id ya ce: Yin rangwami a cikin darare biyu ko uku dan kawar da ƙunci ne da kuma wahala.
  • Abubuwa masu muhimmanci yana kamata a kiyayesu da yin rubutu; domin cewa hakan zai fi sasu tabbatuwa kuma zai fi sa wa a kiyaye haƙƙoƙi.
Sharhi: العربية

أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أنه لا ينبغي لمسلم له شيء يوصي فيه من الحقوق أو الأموال ولو كانت قليلة، أن يبيت ثلاث ليال، إلا ووصيته مكتوبة عنده. قال عبد الله بن عمر رضي الله عنهما: لم أبت ليلة منذ سمعته صلى الله عليه وسلم قال ذلك إلا وعندي وصيتي.

  • مشروعية الوصية والمبادرة إليها، بيانًا لها، وامتثالًا لأمر الشارع فيها، واستعدادًا للموت، وتبصُّرًا بها وبمصرفها، قبل أن يشغله عنها شاغل.
  • الوصية: معناها العهد، وهي أن يَعهد الإنسان بعد موته لشخص في تصريف شيء من ماله، أو يَعهد لشخص بالنظر على أولاده الصغار، أو يعهد لشخص في أي شيء من الأعمال التي يملكها بعد موته.
  • الوصية ثلاثة أقسام: 1- مستحب، وهي الوصيَّة بشيء من مالِه يُصرف في سبيل الخير، والإحسان؛ ليصل إليه ثوابه بعد وفاته، 2- وواجب، وهي الوصيَّة بما عليه من حقوق، سواء كانت هذه الحقوق لله تعالى، كزكاة لم يُخرجها، أو كفَّارة، ونحوها مما يجب عليه بأصل الشرع، أو كانت هذه الحقوق للآدميين؛ كالدَّيْن، وأداء الأمانات، 3- ومحرَّمة، إذا زاد في وصيته على الثلث من ماله، أو إذا أوصى لوارث.
  • فضل ابن عمر رضي الله عنهما، ومبادرته إلى فعل الخير، واتباع الشارع الحكيم.
  • قال ابن دقيق العيد: والترخيص في الليلتين والثلاث دفع للحرج والعسر.
  • الأشياء المهمة ينبغي أن تضبط بالكتابة؛ لأنها أثبت وأحفظ للحقوق.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari