Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ بْنِ مِحْصَنٍ الْأَنْصَارِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ أَصْبَحَ مِنْكُمْ مُعَافى فِي جَسَدِهِ، آمِنًا فِي سِرْبِهِ، عِنْدَهُ قُوتُ يَوْمِهِ، فَكَأَنَّمَا حِيزَتْ لَهُ الدُّنْيَا».
Fassara
Daga Ubaidullahi ɗan Mihsan al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya wayi gari daga cikinku lafiyayye a cikin jikinsa, kuma amintacce a cikin jama'arsa (ko ransa), kuma yana da abin cin yininsa, to kamar an tattaro masa duniya ne».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa yaku musulmai duk wanda ya wayi gari a cikinku yana mai lafiyayye kuɓutacce a cikin jikinsa daga illoli da cututtuka, kuma yana amintacce a cikin ransa da iyalansa da hanyarsa ba ya tsoro, kuma yana da isasshen abin cin yininsa na halal; to kamar an tattara masa duniya ne gabaɗayanta.
Fa'idoji
- Bayanin larurar buƙatuwar mutum ga lafiya da aminci da kuma abinci.
- Ya wajaba akan bawa ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - kuma ya gode maSa akan waɗannan ni'imomin.
- Kwaɗaitarwa akan wadatar zuci da kuma gujewa duniya.
Sharhi: العربية
أخبر النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنه من أصبح منكم أيها المسلمون صحيحًا سالمًا في بدنه من العلل والأسقام، آمنًا في نفسه وأهله وعياله وطريقه غير خائف، عنده كفاية قوت يومه من الحلال؛ فكأنما جُمعت له الدنيا بأسرها.
- بيان ضرورة حاجة الإنسان إلى العافية والأمن والقوت.
- على العبد أن يحمد الله تعالى ويشكره على هذه النعم.
- الترغيب بالقناعة والزهد في الدنيا.